Juyin mulki 8 da aka yi cikin shekaru 3 a Afirka

0
119

Da sanyin safiyar yau Laraba ne, wani gungun Sojojin Gabon suka bayyana a gidan talabijin din kasar tare da sanar da kwace mulki baya ga soke sakamakon zaben da ya nuna Ali Bongo Ondimba a matsayin wanda ya lashe, juyin mulkin da ke matsayin karo na 8 cikin kasa da shekaru 3 a kasashen yammaci da tsakiyar Afrika.
Kafin shekarar 2020 da juyin mulkin ya dawo, Afrika ta yi kokarin sauya matsayar kasancewa nahiya mafi fuskantar juyin mulki a tarihin Duniya, sai dai masana na alakanta tsanantar ayyukan ta’addanci da kuma cin hanci da rashawa a matsayin abin da ya dawo da matsalar a kasashen na yammaci da tsakiyar Afrika.

Gabon

Yau Laraba 30 ga watan Agusta ne sojojin suka yi juyin mulki a Gabon duk da cewa har zuwa yanzu ba a kai ga bayyana sunan wanda ya jagoranci kifar da gwamnatin ta Bongo ba.

Nijar

Nijar ce kasa ta baya-bayan nan da aka fuskanci juyin mulki inda a ranar 26 ga watan Yulin da ya gabata, inda Sojoji suka hambarar da gwamnatin Bazoum Mohammed, inda har zuwa yanzu ake ci gaba da kai ruwa rana wajen ganin lallai an saki shugaban baya ga kafa gwamnatin rikon kwarya gabanin mika mulki ga farar hula.

Tun farko Sojojin na Nijar sun yi tayin mulkin shekaru 3 suna jagoranci gabanin mika mulki amma kungiyar ECOWAS ta yi watsi da shi.

Burkina Faso

Baya ga Nijar sai Burkina Faso wadda a watan Janairun shekarar 2022 Sojoji suka kifar da gwamnatin Roch Kabore saboda gazawarsa wajen yaki da ta’addancin da ya addabi kasar, juyin mulkin da ya gudana karkashin jagorancin Laftanal Kanal Paul-Henri Damiba gabanin Kyaftin Ibrahim Traore ya kwace iko da kasar a watan Satumban bara a wani sabon juyin mulki na daban.

Ko a watan Satumban 2021 Kanal Mamady Doumbouya ya jagorancin juyin mulkin Guinea da ya kai ga hambarar da gwamnatin Alpha Conde, shekara guda bayan tsohon shugaban ya sauya kundin tsarin mulkin kasar.

Chadi

Har zuwa yanzu Sojoji ke ci gaba da jan ragamar Chadi bayan kisan shugaba Idriss Deby Itno a fagen daga yayin gwabza fada da ‘yan tawayen kasar a watan Aprilun shekarar 2021, lamarin da ya bai wa dan sa Janar Mahamat Idriss Deby damar ci gaba da jan ragamar kasar karkashin mulkin rikon kwarya.

Mali

A watan Agustan 2020 ne Sojojin Mali karkashin jagorancin Kanal Assimi Goita suka hambarar da gwamnatin Ibrahim Boubacar Keita amma ya mika mulkin rikon kwarya ga Kanal Bah Ndaw mai ritaya, gabanin ya sake wani juyin mulkin na daban a watan Mayun 2021.

Har zuwa yanzu Assimi Goita ke ci gaba da jan ragamar kasar karkashin mulkin rikon kwarya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here