Juyin mulkin Gabon: Annoba ta tunkaro Afirka – Tinubu

0
202
Tinubu
Tinubu

Shugaban kasar Najeriya ya bayyana cewa yana bin halin da ake ciki a Gabon “cikin damuwa” sakamakon juyin mulkin da sojoji suka sanar a yau Laraba.

Tinubu, wanda shi ne shugaban Æ™ungiyar Ecowas – ta raya tattalin arzikin Æ™asashen Afirka ta Yamma – ya ce yana duba hanyoyin da zai mayar da martani tare da sauran shugabannin Afirka.

Da yake ba da misali da juyin mulkin baya-bayan nan, Tinubu ya ce “annoba” ta kama Afirka, kamar yadda mai magana da yawunsa Ajuri Ngelale ya bayyana.

A ranar Laraba sojoji a Gabon suka sanar da ƙwace mulki kuma suka yi wa Shugaba Ali Bongo mai shekara 64 ɗaurin talala.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here