Legas za ta kaddamar da jirgin kasa mai zirga-zirga a cikin gari

0
131
Jirgin kasa
jirgin kasa

Gwamnatin jihar Legas ta sanar da cewa rukunin farko na sufurin jirgin ƙasa da zai yi zirga-zirga a cikin birnin Ikko mai taken Blue Rail Line zai fara aiki ranar Litinin 4 ga watan Satumba.

Manajar darakta a hukumar kula da sufuri a ƙwaryar birnin Legas (LAMATA), Misis Abimbola Akinajo ce ta sanar da haka a tashar jirgin ƙasa ta Marina ranar Laraba, inda ta nunar cewa jirgin farko zai tashi ne da misalin ƙarfe 9 na safe, inda Gwamna Babajide Sanwo-Olu zai kasance a cikin jirgin tare da sauran fasinjoji daga Marina zuwa tashar Mile 2.

Sanarwar na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin jihar Legas ta gayyaci ‘yan jarida waɗanda suka zagaya a cikin jirgin ƙasa mai suna Lagosmetro.

Misis Abimbola Akinajo ta bayyana cewa a cikin mako huɗu na farko jirgin ƙasa mai amfani da kwal zai riƙa zirga-zirga tsawon sa’a 12.

Daga nan kuma sai jirage masu tafiya da lantarki su fara aiki da jigila 76, kuma an yi ƙiyasin cewa jiragen ƙasa za su riƙa ɗaukar fasinjoji tsakanin 150,000 ko 175,000 a kullu yaumin.

Jiragen ƙasa za su riƙa sufuri ne tun daga ƙarfe 5:30 na safe har zuwa ƙarfe 11 na dare.

Misis Abimbola Akinajo ta ce jirgin ƙasan zai riƙa tsayawa ne tsawon minti ɗaya da rabi kawai a kowacce tasha.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here