Mutumin da ya zana tutar Najeriya ya rasu

0
145

Michael Taiwo Akinkunmi, dattijon nan da ya zana tutar Najeriya, ya rasu a ranar Laraba, yana da shekara 87 a duniya.

Dan marigayin, Akinkunmi Samuel, ne ya sanar da rasuwar mahaifin nasa a Facebook.

“Hakika rayuwa mai shudewa ce; cikin jimami ina sanar da rasuwar mahaifina. Da fatan za ka huta babana! Michael Taiwo Akinkunmi (OFR). Babban mutum ya tafi,” cewar dan nasa.

Gwamnati ta ba Akinkunmi fam 100 a lokacin da aka zabi zanensa a matsayin tutar Najeriya.

Haka kuma an karrama shi da lambar yabo ta lambar yabo ta Gwamnatin Tarayya wanda tsohon Shugaban Kasa, Goodluck Jonathan ya ba shi.

An haife shi a ranar 10 ga watan Mayu 1936, ya fito ne daga yankin Owu, mahaifar tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo da ke Abeokuta a Jihar Ogun.

Ya halarci Makarantar Sakandare ta Baptist Day da ke Ibadan a Jihar Oyo, inda ya yi karatun firamare a makarantar Grammar ta Ibadan.

Bayan ya yi aiki na shekaru da dama, ya je kasashen waje don karanta aikin injiniyan aikin gona a Kwalejin fasaha ta Norwood.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here