Sojojin Gabon sun kama dan hambararren shugaban kasar da laifin cin amanar kasa

0
146

An kama daya daga cikin ‘ya’yan hambararren shugaban kasar Gabon Ali Bongo Ondimba da laifin “cin amanar kasa” bayan juyin mulkin da ya auku.

Sojojin sun bayyana cewa, shugaba Ali Bongo na kulle a gidansa tare da iyalansa da kuma wasu ‘yan uwansa baki daya.

“Shugaba Ali Bongo yana tsare a gida tare da iyalansa da likitocinsa,” inji wata sanarwa da aka fitar a gidan talabijin na kasar ta Gabon.

Sojojin sun yi juyin mulkin ne da sanyin safiyar Laraba, inda suka soke zaben da aka gudanar a ranar Asabar, wanda aka ayyana Bongo a matsayin wanda ya lashe zaben kasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here