Yadda FCTA ta rusa kasuwar dare da ke Asokoro a Abuja 

0
262

Jami’an hukumar babban birnin tarayya Abuja FCTA, a ranar wannan Talatar sun rusa wata haramtacciyar kasuwa mai suna “Kasuwan Dare”, wacce ta kasance maboyar gaggan masu laifi da masu sayar da muggan kwayoyi a Asokoro, Abuja.

Kasuwar ta kasance akan titin Hassan Musa Katsina, kusa da Kpaduma II a Asokoro Extension, Abuja.

Daraktan sashen kula da cigaban birnin, Mista Mukhtar Galadima, ya bayyana cewa haramtacciyar kasuwar ta zamanto barazana ga mazauna yankin da masu wucewa.

Ya kara da cewa, bata-gari da ke gudanar da ayyukansu a yankin suna yin illa ga mutanen muhallin baki daya, inda ya kara da cewa, hukumar ba za ta lamunta ba a ci gaba da hakan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here