Yadda rikici kan dakatar da Kwankwaso a NNPP ke ci gaba da gigita jam’iyyar

0
169

Dambarwa ta kaure a Jam’iyyar NNPP mai hamayya a Nijeriya bayan wasu ‘yan Kwamitin Amintattunta sun yi ikirarin dakatar da dan takararta na shugaban kasa a zaben 2023 Sanata Rabiu Kwankwaso.

A taron da Kwamitin ya gudanar a birnin Legas ranar Talata, ya ce an dakatar da Sanata Kwankwaso tsawon wata shida kan zargin yi wa jam’iyyar zagon-kasa wato anti-party.

Sai dai bangaren Sanata Kwankwaso ya musanta wannan zargi yana mai cewa wasu ne suka dauki nauyin mutanen da suka yi ikirarin dakatar da shi daga jam’iyyar.

‘Ba tare da izini ba’

Da yake yi wa manema labarai jawabi a karshen taron da aka yi ranar Talatar, Sakataren Kwamitin Amintattun Babayo Muhammed Abdullahi, ya zargi Kwankwaso da yin mu’amala da shugaban Nijeriya Bola Tinubu da ‘yan takarar shugaban kasa na PDP da Jam’iyyar Labour Atiku Abubakar da Peter Obi, ba tare da izinin kwamitin ba.

Abdullahi ya ce an warware yarjejeniyar da aka kulla kafin zaben bana, tare da Kungiyar Kwankwasiyya, da kuma kungiyar National Movement (TNM), da kungiyar kasa ta masu tura kaya waje, wato National Association of Government Approved Freight Forwarders (NAGAFF) kan hada-gwiwa a jam’iyyar.

“Mun dakatar da shi ne bisa dogaro da cewa ya saba wa tsarin mulkin NNPP, inda ya nuna rashin ladabi da sanin ya kamata ga bangaren Kwamitin Gudanarwar jami’iyyar.

“Kwamitin Amintattun ya yanke cewa kwakkwarar hujjar da ta bayyana ta tabbatar da Kwankwaso yana yin zagon-kasa ga jam’iyyar inda yake tattaunawar siyasa da Shugaban Nijeriya, da Atiku Abubakar da Peter Obi, ba tare da izinin kwamitin amintattun ba.

“Wannan ne ya janyo masa dakatarwar watanni shida, kafin a samu rahoton bincike na Kwamitin Ladabtarwa,” in ji Abdullahi.

‘Ba gaskiya ba ne’

Amma a tattaunawa da TRT Afrika, Injiniya Buba Galadima, jigo a jam’iyyar ta NNPP ya musanta cewa an dakatar da Sanata Kwankwaso.

Ya kara da cewa shi ne Sakataren Kwamitin Amintattun Jam’iyyar don haka babu wani mataki da za a dauka ba tare da saninsa ba.

“Amma kun san dai ni ne sakataren BOT ko, to wane sakataren ne daban fadi wannan sanarwar ba tare da ni na sani ba?, Buba ya shaida wa TRT Afrika.

“Sannnan mu nawa ne ma ‘yan Kwamitin Amintattun gaba daya? Mu biyu ne fa, ni da Ciyaman, sauran ba a ma kai ga tattara su a amince da shigarsu ba a tukunna.”

A cewar Buba, wasu ‘yan siyasa ne suka dauki nauyin mutanen da suka yi ikirarin dakatar da Sanata Kwankwaso.

“Wasu bara-gurbin ‘yan siyasa ne da ke son ganin bayan Sanata Kwankwaso suka kitsa wannan shirme kuma ba za su yi nasara ba.

“A yanzu a arewacin Nijeriya babu wanda ya tsole wa mutane ido irin Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso,” in ji Buba Galadima.

Shi ma shugaban riko na jam’iyyar NNPP Abba Kawu Ali ya musanta ikirarin dakatar da dan takararsu na shugaban kasa a zaben 2023, kamar yadda gidan talbijin na kasa a Nijeriya NTA ya rawaito.

Sabbin nade-nade

NNPP ta nada sababbin jami’ai karkashin shugabancin Dr. Agbo Major a matsayin shugaban jam’iyyar na rikon kwarya da Mr Ogini Olaposi a matsayin Sakatarenta da wasu mutum 18.

Shugaban rikon jam’iyyar ya ce tawagarsa za ta fara aiki nan-take ta hanyar magance matsalar da ta da ta biyo bayan dakatar da mambobin Kwamitin Gudanarwar Jam’iyyar.

Dr. Agbo Major ya ce kofar jam’iyyar za ta ci gaba da zama a bude ga kowa. Ya nemi mambobin jam’iyyar da wani dalili ya sa suka bar jam’iyyar cewa su dawo cikinta.

Ya kuma kara da cewa, “Ba mu da niyyar rufe wa kowa kofa, ko haramta wa kowa shigowa. Muna so mu tabbatar da cewa mun ci gaba da zama kan turba da akidar kishin al’umma.”

Wannan taro na musamman ya samu halartar sabbin mambobin Kwamitin Gudanarwar jam’iyyar na kasa, daga fadin Nijeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here