‘Al’umma da dama kallon kaskanci sukeyi wa me sana’ar garuwa’ – Tukur Mai Dawainiya

0
153
Tukur Mai Dawainiya
Tukur Mai Dawainiya

Daga Abdurrahman Adam

Kamar yadda rayuwa ke tafiyar da lokuta hakanan take bijirowa da bijire-bijire da dama ga al’umma.

Wadansu sai su samu sa’ar lokuta masu tafiya bisa tafarkin dace da muradansu wasu kuma akasin haka.

A wata tattaunawa ta musamman da Daily News 24 Hausa, Malam Hamza Tukur, dan shekara 30 mai sana’ar garuwa ya magantu kan sha’anin rayuwarsa.

Ya shaida mana cewa yana zaune ne a Zangon Dakata karamar hukumar Ungogo Kano, Najeriya.

Da wannan kasuwancin nasa yake yake daukar nauyin duk wata dawainiyarsa da iyayensa dama yan uwansa baki daya.

Tukur Mai Dawainiya
Tukur Mai Dawainiya

Tattaunawar ta kasance kamar haka;

“Sunana Malam Hamza Tukur, ni Dan jihar Kano ne, a Zangon dakata nake zaune a karamar hukumar Ungogo.

Ni kadai nake gudanar da rayuwata domin har zuwa yanzu bani da aure, Kuma wannan sana’ar ta Garuwa da ita na dogara, ita ke biya min bukatuna da na iyayena dama yan uwana.

Wannan sana’ar tawa na kai shekara 11 a cikinta da ita nake sayen tufafi da kayan more rayuwa da duk kadarorina wadanda nake saya na jefar, na samu alkhairai dayawa sabili da wannan sana’a.

Tukur Mai Dawainiya
Tukur Mai Dawainiya

Zuwa nan da wani lokaci idan na kuma samun nutsuwa zan ci gaba da karatuna sannan na gina gida daga bisani kuma na yi aure.

Sana’ar nan tamu tana da sirri matuka amma kuma cike take da kalubale domin sai an jure sosai an yi hakuri.

Kamar irin lokacin damina aiki baya garawa sosai, haka zalika wasu jama’ar idan suka ganka a cikin irin wannan sana’ar za su ke kallonka a kaskance, za ake ganin kamar baka da hankali baka san komaiba wasu lokutan ma har kyamatarka ake.

Duk lokacin da mutane suka nuna min irin haka nakan ji rashin dadi sosai, amma sai na danne na bar abun a raina.

Bazan taba mantawa ba lokacin da na shahara wajan tura kurayen garuwa har guda uku.

Ina zuwa can unguwar Rangaza dake kasan unguwar mu ta Zangon Dakata na ciko kuraye 3 na taho da su a tare har zuwa unguwar Rimin Kebe.

Wannan kokarin na tura kuraye uku a tare shine ya sanya har jama’a suke kira na da lakabin ‘Mai Dawainiya‘.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here