Gwamnatin Kano ta dakatar da shugaban asibitin Hasiya Bayero

0
351

Gwamna Abba Kabir na jihar Kano ya dakakatar da shugaban Asibitin Hasiya Bayero, Dakta Yunusa Sunusi biyo bayan ziyarar ba zata da Gwamnan ya kai asibitin da tsakar dare.

Gwamnan ya bada umurnin gyara da daidaita yanayin halin da wani bangaren asibitin ke ciki amma shugaban ya nuna halin ko-in-kula.
Dakta Yunusa, ya gaza tattaro kan ma’aikatansa, sannan ya kasa aiwatar da manufofin gwamnati na ganin likita, kula da marasa lafiya da jinya ba tare da an karbi ko kobonsu ba.

Gwamnan ya bayar da umarnin a gaggauta tura Dakta Ibrahim Ibn Muhammad, kwararre a bangaren likitanci domin maye gurbin Dakta Yunusa da aka dakatar, sannan ya tura manyan lokitoci biyu, Dakta Jamila Sani da Dakta Aisha Yahaya domin kula da asibitin kwararru da ke asibitin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here