Gwamnatin jihar Kano ta jam’iyyar NNPP ta yi ikirarin cewa tsohuwar gwamnatin da ta gabata ta jam’iyyar APC, ta bar mata gadon matsaloli masu tarin yawa a barayin ilimi ilimi.
A cewarta a yanzu haka akwai makarantun firamare 400 da suke da malamai dai-dai a shiyyar arewacin jihar, baya ga rashin tebura da kujerun zama na dalibai da dai sauran matsaloli masu hana makaranta gudana.
Sai dai tsohuwar gwamnatin jihar ta Kano, ta ce hangen dala sabuwar gwamnatin jihar ta yi wa lamarin, domin kuwa batun wadannan matsalolin ba wai wani abu ba ne a lullube.
Wannan korafi ya fito ne daga bakin Umar Haruna Dogowa, kwamishinan ilimi na jihar Kanon, wanda ya ce tarin matsalolin ilimi da gwamnatinsu ta gada yana da dimbin yawa, kuma sun gano hakan ne bayan binciken da suka gudanar:
“Mun gano cewa makarantun firamare da ke Kano ta arewa, kananan hukumoi 13, akwai makarantun 400, wadanda malami dai-dai ne a ciki, baya ga tababbarewar gine-gine,” in ji shi.
Kwamishinan ya ce akwai wata makaranta a Dawanau da take da dalibai fiye da dubu biyar amma ba bu kujerun zama kuma ba bu ban daki a cikin makarantar.
A cewarsa akwai wata makaranta a cikin gari inda malamai suke zaune a kasa.
Haka kuma akwai wata makaranta da ke kusa da kofar Nasarawa wadda ke da ajujuwa sama da 20 amma dalibai mata na zaune a kasa saboda rashin kujeru.
Sai dai kwamishinan ilimin na jihar Kano, ya bayar da tabbacin sun dauki matakan warware wadannan matsalolin da ya ce sun tarar:
“Za mu rage yawan ma’aikata da ke zama a ofishoshi in da zamu kai su makarantu, za mu tabbatar mun dauki malamai suke duk inda suke, wadanda ke zaman kashe wando, domin su inganta wannan harka ta ilimi,” in ji shi.
Sai dai kuma Sanusi Sa’idu Kiru, tsohon kwamishinan ilimi a zamanin gwamnatin jihar Kanon da ta gabata, ya ce sun yi iya bakin kokari, wajen shawo kan dimbin matsalolin da ke cunkushe a bangaren na ilimi.
“Lokacin da aka dauki ma’aikata dubu goma da dari takwas malaman makaranta a kwanakin baya, cewa suka yi siyasa ce,” in ji shi.
Sai dai tsohon kwamisinan ilimin ya yi ikirarin cewa gwamnatinsa ta zartar da wata doka wadda ta yi tanadi a kan yadda za a rike makarantu tare da tabbatar da cewa ana samar mu su da inganttatun kayan aiki.