Juyin mulki: Za a rantsar da Janar Brice Nguema na Gabon ranar Litinin

0
173
Gabon-Brice-Oligui-Nguema

Shugabannin da suka yi juyin mulki a Gabon sun ce ranar Litinin za a rantsar da shugaban gwamnatin riƙon ƙwarya na ƙasar, Janar Brice Oligui Nguema.

Sun kuma buƙaci kwantar da hankulan al’ummar duniya ta hanyar yi musu alƙawarin cewa za su mutunta dukkan alƙawurran da Gabon ta ɗauka ciki har da biyan basukan da ke kanta.

Wannan na zuwa ne yayin da Majalisar tabbatar da Tsaro da Zaman Lafiya na Tarayyar Afirka ke gudanar da taro a yau Alhamis, don tattauna batun juyin mulkin Gabon na ranar Laraba.

Shugabannin juyin mulkin sun ce za a rantsar da Janar Nguema ne a gaban Kotun Tsarin Mulki ta Gabon ranar Litinin.

Wani magana da yawun sojojin juyin mulkin ya faɗa a tashar talbijin ta ƙasar cewa sannu a hankali za su kafa cibiyoyin gwamnati za su gudanar da harkokin mulki.

Ƙungiyoyin ƙasashen duniya kamar Tarayyar Afirka na dako su ji tsawon lokacin da shugabannin sojin ke da niyyar kwashewa a kan karagar mulki, kafin su damƙa al’amura a hannun fararen hula.

Yayin sanar da juyin mulkin a jiya Laraba, sojojin sun kuma soke sakamakon zaɓen da ya bai wa Ali Bongo nasara.

A yanzu, ƙawancen ‘yan adawa na kira da a kammala ƙidaya ƙuri’un da aka kaɗa, don ayyana ɗan takarar a matsayin wanda ya yi nasara. Yiwuwar ganin hakan ta tabbata dai a Gabon yanzu, ƙalilan ce.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here