Ko kun san sabon shugaban mulkin sojin Gabon?

0
172

Jagororin juyin mulki a Gabon sun ayyana shugaban dakarun da ke tsaron fadar shugaban kasa, Janar Brice Oligui Nguema a matsayin shugaban rikon kwaryar kasar bayan sun hambarar da gwamnatin Ali Bongo Ondimba kamar yadda wata sanarwar da suka fitar ta kafar talabijin ta bayyana.

Sojojin sun ce, Nguema zai jagoranci mika mulki ga farar hula tare da maido da cibiyoyin gwamnatin kasar.

Su dai wadannan sojoji da suka fito daga masu tsaron fadar shugaban kasar Gabon, sun sanar da juyin mulkin ne a daidai lokacin da ake takaddama dangane da sahihancin zaben da aka yi a karshen mako, wanda hukumar zabe ta ce shugaba Ali Bongo ne ya samu nasara. 

Ko wane ne Janar Brice Oligui Nguema?

An wayi gari Nguema ya zama daya daga cikin manyan masu fada-a-ji a Gabon. Mahaifinsa soja ne, sannan ya samu horon soji a Kwalejin Horas da Sojoji ta Meknes da ke kasar Morocco.
Nguema ya rike mukamin babban dogarin Bongo, sannan ya zama kwamandan sojojin da ke tsaron fadar shugaban kasa a zamanin mulkin Omar Bongo wanda ya rasu a shekarar 2009.

Lokacin da Ali Bongo ya gaji mahaifinsa kan karagar mulki a cikin watan Oktoban shekarar 2019, aka tura Nguema zuwa kasashen Morocco da Senegal domin gudanar da aikin diflomasiyya.

Bayan shekaru 10, Nguema ya zama shugaban masu tsaron fadar shugaban kasar Gabon, yayin da ya taka rawa wajen samar da tsare-tsaren tsaurara tsaro ga shugaban kasa.

Baya ga kwarewarsa ta soji, Nguema ya kasance dan kasuwa wanda ke cikin da’irar attajiran da suka mallaki miliyoyin kudi a Gabon.

Wani bincike da Kungiyar ‘Yan Jarida Masu Bincike Kan Miyagun Laifuka a Duniya ta gudanar a shekarar 2020 kan kadarorin da iyalan Bango suka mallaka a Amurka, ya nuna cewa, Nguema ya zuba hannayen jari a cikin wani rukunin gidaje, inda ya yi ta biyan kudin sannu a hankali.

‘Yan jaridar sun gano cewa, ya mallaki wasu gidaje uku a unguwanni matsakaitan attajirai a Maryland da ke Amurka, inda ya sayi gidajen da kudin da ya zarta dala miliyan 1.

Lokacin da ‘yan jarida suka yi masa tambaya game da wadannan kadarorin, sai Ngumea ya ce musu ” wannan batu ne da ya shafi rayuwarsa shi kadai” a don haka ya kamata a mutunta kadaicinsa a cewarsa.

Mintoci bayan da hukumar zaben Gabon ta sanar da shugaba Ali  Bongo a matsayin wanda ya lashe zaben da ya  gudana ranar Asabar a kasar ne, sojoji suka kifar da gwamnatinsa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here