Shugaban kasar Kamaru ya sauya jami’an tsaron fadar shi bayan juyin mulkin Gabon

0
133
Paul Biya
Paul Biya

Kamar yadda wata majiyar tsaro ta tabbatar, tun a yammacin jiya Laraba, shugaba Biya mai shekaru 90 ya sauya dukkanin masu tsaron lafiyarsa.

A cewar bayanai cikin jami’an tsaron da shugaba Paul Biya ya yi wa garambawul ya kunshi ilahirin wadanda ke bayar da kariya ga fadar shugaban kasa da suka kunshi sojin sama da na ruwa da kuma ‘yan sandan.

Biya wanda ya haura shekaru 40 ya na mulkin kasar ta tsakiyar Afrika, ya hau karagar mulki ne tun a shekarar 1982, inda zarge-zargen take hakkin dan adam suka dabaibaye gwamnatinsa.

Paul Biya na sahun shugabannin Afrika mafiya dadewa a karagar mulki, kazalia mafiya tsufa lura da yadda korafe-korafe suka yi yawa kan lafiyar shi.

Wannan mataki na Biya dai na matsayin cikakkiyar kariya don kauce wa juyin mulkin da jami’an tsaron fadar shugaban kasa suka jagoranta a kasashen Nijar da Gabon.

RFI

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here