Sojojin Nijar sun umarci ‘yan sanda su fitar da jakadan Faransa daga kasar

0
134
Tchiani
Tchiani

Gwamnatin mulkin sojin Nijar ta bayar da umurnin fitar da jakadan Faransa da ke ƙasar, inda ta ce a yanzu ya rasa kariyarsa ta diflomasiyya.

Mista Sylvain Itte ya ci gaba da zama a Nijar duk da cikar wa’adin sa’o’i 48 da aka ba shi na ya fice daga cikin ƙasar a ranar Juma’ar da ta gabata.

Sai dai gwamnatin Faransa ta bayyana cewa jakadanta a Nijar ba zai fice daga ƙasar ba saboda gwamnatin sojojin ba ta da halarci.

Sanarwar da ma’aikatar harkokin wajen Faransa ta fitar na cewa “muna nazari a kan tsaron lafiya da kuma kariya a ofishin jakadancinmu.”

Sojojin dai sun ce sun tuɓe wa jakadan na Faransa rigar kariyar diflomasiyya.

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito wata sanarwar ma’aikatar harkokin wajen Nijar na cewa jakadan “a yanzu ba zai ci moriyar alfarmomi da rigar kariyar da ake bai wa jami’an diflomasiyya masu matsayi irin nasa a ofishin jakadancin Faransa ba”.

“Duk takardun(sa) na diflomasiyya da biza har ma da na iyalansa, an soke su.

A ranar Juma’a cikin makon jiya ne, hukumomin sojin suka bai wa jakadan Faransa wa’adin sa’a 48 don ya bar Nijar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here