An hallaka ‘yan ta’adda 39, an kama 159 a Borno da Yobe

0
111

Sojin rundunar Operation Hadin Kai, sun yi wa wasu ‘yan bindiga kwanton bauna, wanda hakan ya ba su nasarar kashe 39 tare da kama 159 daga cikinsu. 

Kazalika, sojin sun kuma ceto mutane 109 da masu garkuwa suka sace a waje daban-daban.

Daraktan yada labarai na rundunar tsaro Majo Janar Edward Buba, ya shaida wa manema labarai hakan a yau Alhamis shalkwatar rundunar da ke Abuja.

Ya ce, rundunar sojin kasa, ta lashi tokobin ci gaba da dakile masu son yi wa kasar nan zagon kasa na samun ‘yanci.

Ya ci gaba da cewa, jirgin sojin sama ya yi luguden wuta a wani sansanin ‘yan bindiga a dajin Sububu da ke a karamar hukumar Kankara ta Jihar Katsina, inda suka tarwatsa sansanin nasu.

Bugu da kari, ya ce sojin sun kuma yi wa wasu manyan ‘yan ta’addar Boko Haram da na ISWAP kwanton bauna, inda suka kama su, a Gwoza da Tarmuwa da ke a Borno da kuma Yobe.

A cewarsa, hakan ya kuma tilasta wasu daga cikin ‘yan ta’addar mika wuya a Gwoza da ke a jihar Borno, inda a wannan nasara, sojin suka kashe wasu ‘yan ta’addar suma kuma ceto mutanen da suka sace tare da kwato makamai da albarusai.

Bugu da kari, sojin a wani aikin da suka yi, sun hallaka ‘yan ta’adda 11, sun cafke 45 sun kuma ceto mutane 34, tare da kuma kwato makamai da albarusai.

Ya ce, daga cikin makaman sun hada da, bindigun AK-47 shida, bindiga daya kirar HK21, bindiga daya kirar GPMG, bindiga kirar gida guda daya, kunshin albarusai guda 11 da sauransu.

Ya ce, sojin rundunar Operation Safe Haven da ke aiki a Arewa ta Tsakiya, sun kashe ‘yan bindiga biyu sun kuma ceto mutane uku da aka sace tare da kuma kama ‘yan bindiga 15.

Kazalika, ya ce sojin rundunar Operation Delta Safe a mako biyun da suka gabata, sun kama wasu da ake zargin barayin mai ne a yankin Neja Delta da kuma mutane 34 da sarrafa haramtacciyar matatar mai, wadda sojin suka lalata.
Bugu da kari Buba ya sanar da sojin sun kuma dakile yunkurin masu satar mai, tare da kwace kudi Naira miliyan 765.8 a wajensu da kama makamai guda 55 da albarusai guda 96.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here