Gwamnatin Rasha ta musanta zargin da ake yi mata na haddasa yunwa a kasashen Afrika, tana mai cewa, har yanzu tana ci gaba da fitar da hatsi zuwa nahiyar duk kuwa da takunkuman da kasashen yammacin duniya suka kakaba mata.
A cikin watan Yulin da ya gabata ne, Rasha ta fice daga yarjejeniyar da ta cimma ta tsawon shekara guda wadda ta bai wa Ukraine damar fitar da hatsi daga gabar tekun Black Sea duk da hare-haren da Moscow ke kaddamar mata, abin da ya taka rawa wajen samun rahusan farashin kayan abinci a sassan duniya.
A lokacin da aka tambaye shi kan zargin da ake yi wa Rasha na haddasa yunwa a kasashen Afrika, Mai Magana da Yawun Fadar Kremlin Dmitry Peskov ya ce, wadannan zarge-zarge ne marasa tushe ballanta makama kuma an kirkire su ne domin sauya gaskiyar al’amari a cewarsa.
Mista Peskov ya kara da cewa, karancin abinci da hatsi a yankin Afrika sam, ba shi da nasaba da Rasha, hasali ma cewa ya yi, akwai shirin da suka bullo da shi domin tura kayan abinci kyauta zuwa ga kasashe matalauta a Afrika duk da cewa, yarjejeniyar da suka kulla da Ukraine ta daina aiki.
Shugaba Putin ya yi alkawarin aike wa da tan dubu 50 na hatsi kyauta ga kasashe shida na Afrika.