Man da Najeriya ke fitarwa a yanzu ya karu – NNPC

0
143
NNPC Mele Kyari
NNPC Mele Kyari

Shugaban Kamfanin Man Najeriya na NNPC Mele Kolo Kyari ya ce kasar a halin yanzu tana fitar da gangar mai miliyan guda da dubu 670, sakamakon sabbin matakan da ta dauka tare da jami’an tsaro na dakile satar man da batagari ke yi.

Kyari ya bayyana cewar wannan gagarumar nasara ce lura da irin matsalolin da aka fuskanta a baya na satar man wanda ya hana Najeriya fitar da adadin da kungiyar OPEC ta ware wa kasar.

Matsalar satar man da ake fuskanta a Najeriya ta yi matukar illa wajen durkusar da bangaren fitar da man da kuma kudaden shigar da kasar ke samu, abin da ke zama babban kalubale ga gwamnati.

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya kaddamar da sabbin sauye-sauye a bangaren samar da man wajen cire tallafin da gwamnati ke zubawa, wanda ya kai dala biliyan 10 a shekarar da ta gabata, kuma a daidai lokacin da gwamnatin Muhammadu Buhari ta kawo karshe.

Kyari ya ce, da gwamnati na ci gaba da biyan tallafin har yanzu, ganin yadda farashin man ya tashi a kasuwannin duniya, da Najeriya za ta kashe abin da ya kai naira triliyan guda kowane wata kafin saukaka wa jama’ar kasar farashin man da suke sha.

Shugaban NNPC ya ce matakin sabuwar gwamnatin ya kuma rage yadda jama’a ke shan man a cikin gida da kashi 30, wato an samu raguwar man da ake sha zuwa lita miliyan 46 bayan cire tallafin da gwamnati ke zubawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here