Gwamnatin Gombe ta yi wa ma’aikatanta da na kananan hukumomi karin albashi

0
143

Gwamnatin Gombe ta yi wa ma’aikatanta da na kananan hukumomi karin N10,000 a kan albashinsu, domin rage musu raadadin cire tallafin mai da Sakamakon janye tallafin man fetur da Gwamnatin Tarayya.

Mataimakin gwamnan jihar, Manasseh Daniel Jatau ya shaida wa taron manema labarai a ofishinsa cewa gwamna Inuwa Yahaya ya amince karin ya fara aiki daga albashin watan Agusta.

Da aka tambaye shi wa’adin daina biyan ƙarin, sai ya ce a yanzu dai ba a ƙayyade lokacin kawo ƙarshen hakan ba.

Gwamnatin Gombe ta yi wa ma’aikatanta da na kananan hukumomi karin N10,000 a kan albashinsu, domin rage musu radadin cire tallafin mai da Sakamakon janye tallafin man fetur da Gwamnatin Tarayya.

Ya yaba da gudumawar da ma’aikata ke bayarwa a jihar, inda ya bayyana su a matsayin ƙashin bayan gudanar da ayyuka da manufofin gwamnati.

Jatau ya ce gwamnan ya yi wa ma’aikata karin ne saboda tausayin halin da su da sauran al’ummar jihar sun shiga, wanda kafin karin albashin ya samar da tallafi daban-daban tun bayan barkewar annobar COVID-19.

A cewarsa, tun bayan cire tallafin man fetur gwamnatin jihar ta ɗauki matakan daƙile illolin hakan ga al’ummar jihar ta hanyar fara raba tallafi ga mutane dubu 30 wadanda a karshe kimanin mutum 420,000 za su ci gajiya a faɗin jihar.

Daga nan sai ya kira yi daukacin al’ummar Jihar Gombe musamman waɗanda har yanzu ba su ci gajiyar tallafin ba, da cewa su ƙara haƙuri, domin za’a ci gaba da ɓullo da karin shirye-shiryen tallafi nan bada jimawa ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here