Tinubu ya dawo da jakadun Najeriya gida

0
208
Tinubu
Tinubu

Ma’aikatar harkokin ƙasashen wajen Najeriya ta ce shugaban ƙasar Bola Tinubu ya mayar da jakadun ƙasar da ke ƙasashen ƙetare.

Cikin wata sanaraw da fadar shugaban kasar ta wallafa shafinta na X da a baya aka fi sani da Twitter, ta ce umarnin ya shafi duka jakadun ƙasar a ƙashen ƙetare, in ban da wakilan ƙasar na dindindin a Majalisar Dinkin Duniya a New York da Geneva, sakamakon babban taron Majalisar da za a yi nan gaba cikin wannan wata.

Hakan na zuwa ne bayan mayar da jakadan Najeriya daga Birtaniya Ambassador Sarafa Tunji Ishola.

Ministan harkokin wajen Najeriya Ambassador Yusuf Maitama Tuggar ya ce an mayar da duka jakadun ne bisa umarnin shugaban ƙasar Bola Tinubu.

“Jakadu a matsayinsu na wakilan ƙasar, suna aiki ne da umarnin shugaban ƙasa, domin kuma shi ne ke da ikon aikawa da mayar da jakadun zuwa ga kowacce ƙasa”, kamar yadda sanarwar ma’aikatar harkokin ƙasashen wajen ta bayyana.

Tun da farko shugaba Tinubu ya mayar da jakadan Najeriya a Birtaniya Ambassador Sarafa Tunji Ishola wanda tsohon shugaban ƙasar Muhammdu Buhari ya naɗa a watan Janairun 2021.

Cikin takardar umarnin mayar da jakadan, ministan harkokin ƙasashen wajen Najeriya ya ce ”Ina amfani da wannan dama wajen bayyana godiyar shugaban ƙasa bisa aikin da ka yi a matsayin jakadan Najeriya a Birtaniya”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here