Gwamna Raɗɗa ya raba N20m ga iyalan ‘yan sintirin da suka rasu a yaki da ‘yan bindiga

0
192

Gwamnatin Jihar Katsina ƙarƙashin jagorancin Malam Dikko Umar Raɗɗa ya ware kuɗi naira miliyan 20 domin tallafawa iyalan ‘yan sintiri da suka rasa rayukansu a lokacin fafatawa da ‘yan bindiga.

Da yake ƙaddamar da bada wannan tallafi, sakataren gwamnatin jihar Katsina Alhaji Abdullahi Garba Faskari ya bayyana cewa, anyi wannan tsari da kyakkyawar niyya domin rage radadin rashin da iyalan jami’an tsaro da ‘yan sintiri suka yi.

A cewar sa wannan ɗaya ne daga cikin tarin tsare-tsaren da wannan gwamnati take da shi na nuna kauna da tausaya wa ga iyalan waɗanda suka rasa iyalansu da kuma waɗanda suka samu raunuka.

 Sakataren gwamnatin jihar Katsina ya ƙara da cewa wannan yana daga cikin alkawarin da gwamna Malam Dikko Umar Raɗɗa ya ɗauka akan wannan matsala ta tsaro wanda ya ce kullum da abin yake kwana da shi yake tashin.

“Idan jama’a ba su manta ba, gwamna Malam Dikko Raɗɗa ya bayyana cewa idan kuɗin jihar Katsina za su ƙare akan matsalar tsaro, to zai tunkare ta tsakaninsa da Allah, kuma ku shaida ne, kwana nan ya amince da kashe Naira biliyan dubu 7.8 akan wannan matsala.” Inji Faskari

Haka kuma ya yi kira ga jama’a da su taimakawa jami’an tsaro da bayanan sirri wanda zai taimaka wajan kawo ƙarshen wannan matsala, sannan ya ƙara jaddada cewa kofar wannan gwamnati a buɗe take domin bada shawara musamman akan sha’anin tsaro.

Shina yake jawabi, mai taimakawa Gwamna Raɗɗa akan waɗanda bala’in ‘yan bindiga ya shafa. Alhaji Sa’idu Ibrahim Danja ya bayyana cewa duk jami’an tsaron ‘yan sintiri sauransu gwamnati ke ɗaukar nauyin yi masu magani idan suka sami raunuka.

A cewar sa yanzu haka akwai jami’an tsaro guda 4 da jama’ar gari 32 da suke kwance a asibitin koyarwa ta Katsina da kuma asibitin Ƙashi kuma gwamnatin Malam Dikko Umar Raɗɗa ke ɗaukar nauyin yi masu magani.

Ya ƙara da wannan naira miliyan 20 da aka ware an tsara yadda za a rabawa iyalan waɗanda wannan lamari ya shafa su talatin da uku (33) inda ya ce kowace mutum za a baiwa iyalansa naira dubu 500 da kuma iyalan wani jami’in soja da ya rasa ransa za a bashi naira miliyan ɗaya.
” Haka kuma muna da jami’an tsaro guda goma da suka samu raunuka wanda kuma za a baiwa kowanne su Naira dubu ɗari biyu da hamsin (250) domin su cigaba da tallafawa iyalan su” inji

Daga ƙarshe ya bayyana cewa waɗannan kuɗaɗen da aka ba su ba wai diyya ba ce, tallafi daga gwamna Malam Dikko Raɗɗa kuma wata hanya ce ta ƙara ƙarfafa jami’an tsaro akan wannan aiki na sadaukarwa da suke yi ba dare ba rana.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here