Gwamnatin tarayya za ta kafa cibiyoyin agaji a kananan hukumomi 774 don rage talauci

0
224
Ministar Harkokin Agaji da RagAe Talauci Betta Edu, ta ce ma'aikatarta za ta gina cibiyoyiin agaji a dukkan ƙananan hukumomin Najeriya 774.

Ministar Harkokin Agaji da Rage Talauci Betta Edu, ta ce ma’aikatarta za ta gina cibiyoyiin agaji a dukkan ƙananan hukumomin Najeriya 774.

A cewarta, cibiyoyin za su yi aiki ne a matsayin mataki na korar talauci a hankali, kuma za a ajiye kayan abinci ne da aka samar a cikin gida.

“A ƙarƙashin mulkina, ma’aikatar agaji za ta rage talauci ta hanyar ƙirƙirar ayyukan yi, da tura wa masu ƙaramin ƙarfi kuɗi,” in ji ministar lokacin da take magana a gidan rediyon tarayya ranar Asabar.

A watan Agusta ne Bola Tinubu ya rantsar da Edu a matsayin minista bayan ta sauka daga muƙamin shugabar mata ta jam’iyyarsu mai mulki ta APC.

Ana ganin ma’aikatar tata za ta taka muhimmiyar rawa wajen aiwatar da tsare-tsaren gwamnatin na rage wa ‘yan Najeriya raɗaɗin cire tallafin man fetur, wanda ya jawo ninninkawar farashi a faɗin ƙasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here