Hatsarin mota ya hallaka mutum shida a jihar Osun

0
144

Hukumar kiyaye haɗurra a Najeriya ta ce aƙalla mutum shida ne suka rasu sakamakon hatsarin mota da ya afku a jihar Osun da ke kudancin ƙasar.

Kwamandan shiyya, Henry Benamesia, ya ce ababen hawa biyu ne suka yi karo da juna ranar Asabar da misalin ƙarfe 9:44 na dare sakamakon shanyewar birki na ɗaya daga cikinsu, wanda hakan ya jawo mutuwar shida daga cikin fasinjojin.

“‘Yan sanda sun kai gawar mutum biyar asibitin koyarwa na Osun kafin zuwan jami’an hukumar FRSC,” kamar yadda kamfanin labarai na NAN ya ambato Mista Benamesia yana bayyanawa cikin wata sanarwa.

“Ɗaya gawar ta maƙale ne a jikin ɗaya daga cikin motocin, har sai da muka yi amfani da inji kafin mu iya ɓamɓare ta.”

Benamesia ya ce gudun wuce kima da ɗaya daga cikin motocin ke yi ne ya haddasa hatsarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here