Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai halarci taron ƙungiyar ƙasashe masu ƙarfin masana’antu ta G-20.
Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Ajuri Ngelale ya fitar, ya ce Tinubu zai halarci taron ne bisa gayyata ta musamman da firaministan Indiya Narendra Modi ya aika masa.
Mista Ngelale ya ce Tinubu zai bar Najeriya ranar Litinin zuwa birnin Delhi na ƙasar Indiya inda za a gudanar da taron.
Duk da kasancewa Najeriya ba ta cikin ƙungiyar ta G-20, ana sa ran shugaba Tinubu zai yi jawabi a taron.
Sanarwar ta kuma ce a gefen taron shugaba Tinubu zai gabatar da jawabi a wata ganawa da zai yi firaminstan na Indiya, da kuma taron kasuwanci tsakanin ƙasashen biyu da za a shirya.
Manyan ‘yan ƙasuwa da jami’an gwamnatin Indiya da na Najeriya ne za su halarci taron tattaunawar kasuwanci tsakanin ƙasashen biyu.
Ngelale ya ce shugaban Najeriyar zai yi amfani da wannan taro wajen janyo hankalin masu zuba jari na ƙasashen wajen zuwa Najeriya don samar da ayyukan yi tare da sama wa ƙasar ƙarin kuɗin shiga don haɓaka tattalin arzikinta.
Daga cikin jami’an gwamnatin da za su yi wa shugaban rakiya zuwa taron akwai ministan harkokin ƙasashen waje, da ministan kuɗi da na tattalin arziki, da ministar sadarwa, da ministar kasuwanci da masana’antu
Shugaba Tinubu zai koma Najeriya da zarar an kammala taron, kamar yadda sanarwar ta bayyana.