A jamhuriyar Nijar, ana sa ran ƙarin zanga-zanga a birnin Yamai game da neman dakarun Faransa su fice daga ƙasar ta yammacin Afirka.
A jiya Asabar dubban mutane suka yi gangami a wajen sansanin sojin Faransa da ke Yamai.
Akwai dakarun Faransa aƙalla 1,500 a Nijar waɗanda ke yaƙi da masu iƙirarin jihadi a yankin Sahel.
Dangantaka tsakanin Nijar da tsohuwar uwargijiyarta ta ƙara tsami tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi wa Shugaba Mohamed Bazoum a watan Yuli da ya wuce.
A ranar Juma’a shugaban sojin Nijar ya soki matakin ƙin amincewa da gwamnatinsu da Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya yi, yana mai cewa kullum suna magana da Bazoum ta wayar tarho.