Abubuwan da sabon shugaban mulkin sojin Gabon zai yi wa kasar

0
179

Sabon shugaban mulkin sojin Gabon da ya sha rantsuwar kama aiki a wannan Litinin Janar Brice Nguema ya yi alkawarin gudanar da sahihin zabe domin maido da mulkin farar hula duk da cewa, bai tsayar da ranar shirya zaben ba.

Kazalika sabon shugaban ya yi alkawarin yin afuwa ga fursunonin siyasa, yana mai jaddada cewa, juyin mulkin da suka yi, ya ceci Gabon daga zubar da jini bayan gudanar da zaben da ya ce, na cike da murdiya da kurakurai.

A ranar Laraba da ta gabata ne, Oligui wanda shi ne shugaban dakarun tsaron fadar shugaban kasa, ya jagoranci hambarar da gwamnatin Ali Bongo Ondimba wanda iyalansa suka shafe tsawon shekaru 55 suna shugabancin kasar mai arzikin man fetur.

Juyin mulkin na zuwa ne bayan hukumar zabe ta ayyana  Bongo mai shekaru 64 a matsayin wanda ya sake yin nasarar a zaben na shugaban kasa, zaben da ‘yan adawa suka yi watsi da sakamakonsa.

Sabon shugaban na mulkin soji ya nemi hadin-kan daukacin manyan kungiyoyin Gabon domin rubuta sabon kundin tsarin mulkin kasar wanda ya ce, za a rubuta bayan gudanar da kuri’ar jin ra’ayin jama’a.

Oligui mai shekaru 48, sanye da jan kakin soji na musamman, ya ce, zai umarci gwamnatin kasar da za ta zo nan gaba da ta muhimmanta yin afuwa ga fursunonin siyasa tare da saukaka wa mutanen da suka gudu dawowa cikin kasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here