Hukumomi a jihar Kano da ke arewacin Najeriya sun kaddamar da rabon tallafin kayan abinci da na noma ga al’ummar jihar don rage musu raɗaɗin cire tallafin man fetur.
Gwamnatin ta ce ta fara raba shinkafa mai nauyin kilogiram goma-goma da masara ga magidanda, musamman waɗanda suke zaune a karkara.
Abu biyu aka ƙaddamar a yau Litinin, na farko rabon kayan noma da injinan sana’o’in hannu, sai kuma kuma rabon tallafin kayan abinci.
Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya ce sun yi tanadi mai yawa na kayan abincin da suka sayo daga gwamnatin tarayya don tallafa wa mutane musamman mata.
Gwamnan ya kara da cewa daga yau sun ƙaddamar da bayar da tallafin shinkafa buhu 297,000, inda za a ci gaba da raba wa masu ƙaramin ƙarfi a mazaɓu 484 na jihar da ke ƙananan hukumomi 44.
Baya ga wannan kuma, an raba wa mata da maza kayan noma ciki har da taki da injinan ban ruwa da na niƙan masara.