Shugabannin NLC sun yi watsi da hayyatar da gwamnati ta yi musu

0
131

Shugabannin kungiyar kwadago ta Nijeriya NLC sun kaurace wa taron da ministan kwadago da samar da ayyukan yi, Simon Lalong ya kira da nufin hana shiga yajin aikin gargadi na kwanaki biyu da kungiyar ta shirya yi.
 
Wakilin Daily Trust da ke wurin taron, ya rahoto cewa, shugaban kungiyar ‘yan kasuwa (TUC), Festus Osifo ne kawai ya halarci taron da aka shirya da misalin karfe 3 na rana amma aka fara shi da karfe 5:32 na yamma.

A ranar Juma’ar da ta gabata ne kungiyar NLC ta bayyana cewa, duk rassanta da ke fadin kasar nan su fara shirin yajin aikin gargadi na kwanaki biyu daga ranar Talata 5 ga watan Satumba sabida halin kuncin da ‘yan Nijeriya ke ciki a fadin kasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here