Tallafin mai: Rashin cunkoso a titunan Legas asara ce ga Najeriya

0
134

Birnin Legas ya zama daban, kacaniya da hayaniyar da aka san birnin kasuwancin na Najeriya da su sun ragu saboda cire tallafin man fetur.

Tun daga watan Yuni, farashin man fetur ya ninka sau uku, abin da ya jawo hauhawar kuɗin sufuri da kuma tilasta wa wasu ma’aikata yin aiki daga gida.

Akasarin mutane sun daina hawa motocinsu. Saboda ƙarancin fasinjoji, yanzu motocin bas masu launin ɗorawa da ake haya da su na jingine a tashoshi.

Tuni dogayen layukan mota suka ragu sosai a birnin.

Wannan birnin mai yawan al’ummar da aka yi hasashe sun kai miliyan 20 yanzu shuru yake, amma kuma hakan ba abu ne mai kyau ba.

Nutuswar da Legas ya samu ta sa ya yi rashi a ɓangaren tattalin arziki tun bayan da Shugaba Bola Tinubu ya sanar da cire tallafin bagatatan a ƙarshen watan Mayu.

Ya ce Najeriya mai arzikin fetur ba za ta iya ci gaba da biyan kuɗin tallafi ba, wanda ke lashe biliyoyin naira duk wata.

CIre tallafi da kuma cire takunkumin canjin kuɗi ya jawo wa tattalin arzikin ƙasar matsaloli, duk da cewa masana na cewa matakai ne da suka dace, kuma babu inda lamarin ya fi ƙamari fiye da Legas.

Da yawa daga cikin masu ƙananan sana’o’i sun daina, kuma wasu daga cikin mazauna unguwannin wajen Legas da ke shiga birnin don yin ayyuka a kullum sun daina zuwa.

“A baya nakan kashe naira 600 wajen sufuri, sai ya koma 1,000. Zuwa ƙarshen wata sai ka ga na kashe albashina gaba ɗaya a kuɗin zuwa wajen aiki,” a cewar wata mai aikin goge-goge, tana mai cewa dole ta sa ta ajiye aikin.

Tana zaune ne a Ikorodu, wata unguwa mai cunkoso da masu ƙaramin ƙarfi ke zaune.

A baya, tafiyar mai nisan kilomita 41 daga Ikorodu zuwa unguwar masu kuɗi ta Victoria Island kan ɗauki awa biyu zuwa uku a lokacin cunkoson tafiya aiki. Yanzu ba ta fi minti 45 ba zuwa 50.

Sabbin alƙaluma daga hukumar ƙididdiga ta ƙasa sun nuna cewa idan aka kwatanta da wata uku na biyu a shekarar 2022 da na 2023, gudummawar da sufurin titi ke bai wa tattalin arziki ya ragu da kashi 47 cikin 100.


Ganin cewa alƙaluman sun duba wata ɗaya ne kawai tun bayan cire tallafin, akwai yiwuwar lamarin ya fi ƙamari.

Za a fi jin wannan matsin a Legas, birnin da ke da gaɓar ruwa mafi cunkoso kuma wanda shugaban Najeriyar ke alfaharin ya gina shi da kyau.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here