Zaben Najeriya: Shettima ya jagoranci tawagar APC zuwa kotu don sanin matsaya

0
101

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya jagoranci jiga-jigan jam’iyyar APC zuwa kotun daukaka kara wacce za ta yanke hukunci kan zaben shugaban kasa a yau Laraba.

Kotun za ta yanke hukunci kan kararraki uku da ke kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasar da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu.

Kotun ta yanke shawarar yanke hukunci ne yau Laraba biyo bayan sauraron korafe-korafen duka bangarorin da ke kalubalantar sakamakon zaben a watan da ya gabata, kuma kimanin makonni biyu ya rage cikar wa’adin kwanaki 180 da aka kayyade na yanke hukunci kan karar da aka shigar tun a watan Maris.

Shettima a halin yanzu na zaune a gaban kotun tare da wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar APC, kamar shugaban jam’iyyar na kasa, Abdullahi Ganduje; Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila; Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu; Ministan sufurin jiragen sama, Festus Keyamo, da dai sauransu.

Akalla gwamnonin APC hudu ne suka hallara a gaban kotun. Abdullahi Sule (Nasarawa), Biodun Oyebanji (Ekiti), Yahaya Bello (Kogi), Mai Mala Buni (Yobe), Hope Uzodinma (Imo).

Manyan jiga-jigan jam’iyyar PDP karkashin jagorancin Iliya Damagum, mukaddashin shugaban jam’iyyar na kasa, suma sun gurfana a gaban kotu tare da na jam’iyyar Labour.

An girke Jami’an tsaro da dama akan dukkan hanyoyin da za su kai ga zuwa kotun, wadanda aka zabo daga hukumomi daban-daban, da suka hada da sojoji, ‘yansanda, jami’an tsaro na farin kaya (DSS) da kuma Civil Defence.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here