Cikin shekaru 11 Najeriya ta yi asarar tiriliyan 16.25 — Tj Abbas

0
210

Kakakin majalisar wakilan Najeriya, Tajudden Abbas, ya ce, Najeriya ta yi asarar naira tiriliyan 16.25 sakamakon satar danyen mai a tsakanin shekarar 2009 zuwa 2020.

Kakakin ya bayyana haka ranar Alhamis lokacin da yake kaddamar da kwamitin bincike kan satar danyen mai da kuma asarar kudaden shiga da aka gudanar a Abuja.

Abbas ya ce, barazanar satar danyen mai na kara haifar da mummunar nakasu ga albarkatun mai da Nijeriya ke hakowa, inda ya ce, tsakanin kashi biyar zuwa kaso kaso 30 na danyen mai ake asara kullum.

Kakakin ya bayyana cewa, hukumomi da ma’aikatun da suke da alaka da harkar mai irin su NNPC, hukumar NUPRC, ma’aikatar albarkatun mai da sauransu sun ki amsa gayyatar da aka tura musu.

Shugaban kwamitin albarkatun mai na majalisar wakilai, Al-Hassan Ado-Doguwa, ya ce, muddin ba a dauki matakin gaggawa wajen shawo kan wannan matsalar ba, to kuwa Nijeriya za ta iya fuskantar manyan matsaloli a nan gaba.

A cewarsa, hakan na da nasaba da koma-baya ta fuskar kudaden shiga a harkar mai da na iskar gas.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here