Dalilai biyar na korar ƙararrakin Atiku da Obi

0
145

‘Yan Najeriya na ci gaba da tsokaci da faɗar albarkacin bakinsu, bayan kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa ta kori ƙararrakin ‘yan adawa da ke neman a soke cancantar Bola Ahmed Tinubu.

Jagoran adawa a Najeriya, Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP da Peter Obi na jam’iyyar Labour da kuma wata jam’iyya mai suna APM ne suka shigar da ƙara. Suna iƙirarin cewa zaɓen watan Fabrairu cike yake da maguɗi da kura-kurai.

Sai dai a zaman da ta yi na fiye da tsawon sa’a 12 ranar Laraba a kan ƙorafe-ƙorafen, alƙalan kotun biyar ƙarƙashin jagorancin Mai shari’a Haruna Tsammani, sun ce ƙararrakin ba su da tushe balle makama.

Mai shari’ar da sauran alƙalan kotun sun tabbatar da Bola Tinubu, a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban Najeriya na 25 ga watan Fabrairun 2023.

Amma jam’iyyun PDP da LP sun ce ba su yarda da hukuncin ba. ‘Yan takararsu wato Atiku da Peter Obi, ba su halarci zaman kotun ba.

Masana shari’a sun ce ‘yan adawan, suna da damar ɗaukaka ƙara zuwa Kotun Ƙoli a cikin mako biyu.

To amma ko waɗanne hujjoji, kotun sauraron ƙararrakin zaɓen ta dogara da su wajen korar ƙorafe-ƙorafen?

Ga dalilai guda biyar da muka zaƙulo muku:

‘Aika sakamako ta laturoni’

Jam’iyyar LP da ɗan takararta Peter Obi, sun yi zargin tafka maguɗi saboda rashin aika kwafen takardun sakamakon zaɓe nan take ta hanyar laturoni.

Hukumar zaɓe ta INEC ce ta ɓullo da tsarin aika kwafin takardar sakamakon zaɓe ta laturoni da na’urar BVAS a take, da zarar an kammala ƙidaya ƙuri’un da aka kaɗa a rumfar zaɓe, zuwa wani rumbun intanet mai suna IREV. Rumbun da kowa yana iya shiga, ya ga sakamakon da ake aikawa daga sassan ƙasar.

Tsarin amfani da fasahar zamanin dai, zai yi aiki ne kafaɗa-da-kafaɗa da hanyar al’ada ta ɗaukar takardar sakamako a hannu, a kai cibiyar tattara sakamako.

Yin hakan zai tabbatar da tsare gaskiya da yin komai babu rufa-rufa, da kuma toshe kafar zarge-zargen canza alƙaluma.

Sai dai, ba duka sakamakon zaɓen ne, hukumar ta iya ɗorawa a shafin IREV ba, lamarin da ya janyo ƙorafi da zarge-zarge.

To amma, kotu ta ce INEC, hukuma ce mai zaman kanta, kuma tana da ‘yancin cin gashin kanta, sannan tana da hurumi ta tsara wa kanta yadda za ta yi aikinta. Tun daga tantance masu zaɓe har zuwa tattara sakamako, ta hanyar da ta ga dama, kamar yadda dokar zaɓe ta 2022 ta tanada.

Shugaban kotun, Mai shari’a Haruna Tsammani ya ce kundin dokokin zaɓe na 2022, bai tilasta wa INEC ta yi amfani da hanyar laturoni wajen aika sakamako ba.

Na’ura ɗaya da ta zama dole hukumar INEC ta yi amfani da ita, ita ce BVAS, don tantance masu zaɓe.

Kotun ta kuma ce jam’iyyar LP da Peter Obi, ba su da hujjar cewa lallai sai ɗan takarar da ya samu aƙalla kashi 25 cikin 100 na ƙuri’un da aka kaɗa a Abuja, babban birnin Najeriya, kafin a tabbatar masa da nasarar shugabancin ƙasa.

LP dai tana bugun ƙirjin cewa ita ce ta samu ƙuri’u mafi rinjaye a Abuja.

Sai dai, alƙalan kotun sun ce, “Abuja tamkar sauran jihohin Najeriya, ba ta da wani hurumi na musamman”.

‘Laifin safarar ƙwaya a Amurka’

Wani ƙorafi da kotun ta sake yin watsi da shi, shi ne iƙirarin da ‘yan adawar suka yi na cewa kotu a Amurka ta taɓa kama Bola Tinubu da laifin safarar ƙwayoyi da kuma halasta kuɗin haram.

Jam’iyyar LP da Peter Obi sun ce kotu ta taɓa ƙwace wa Bola Tinubu kuɗi dala 460,000 da ke da alaƙa da safarar ƙwaya a Amurka. Sun ce wanda aka taɓa samu da irin wannan laifi, ba shi da nagartar da zai jagoranci Najeriya.

Jam’iyyar da ɗan takararta, amma ba su iya gabatar wa kotu da hujjojin cewa an yi wa Tinubu tuhumar aikata babban laifi ba, ko kuma cewa an kama shi da laifin da suka yi iƙirari.

Mai Shari’a Tsammani ya ce don kotunsu ta yi watsi da ƙorafin.

Ya ce masu ƙorarin ba su iya gabatar da wata hujja da ke nuna cewa kotu ta ɗaure Tinubu a kan wannan zargi da suka yi ba.

Haka zalika, alƙalin ya ce lauyoyin Tinubu sun gabatar da wata wasiƙa daga ofishin jakadancin Amurka da ke cewa babu sunan mutumin da suke karewa a cikin rijistar waɗanda kotu ta taɓa samu da laifi a ƙasar.

Don haka, kotun ta ce bisa la’akari da tsarin mulki, iƙirarin da masu ƙorafi suka yi, bai isa zama hujjar soke cancantar takarar Tinubu ba.

‘Tinubu ba cikakken ɗan Najeriya ba ne’

Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa kuma, ta yi watsi da buƙatar ɗan takarar jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar wanda ya nemi a soke nasarar Tinubu, saboda ya mallaki takardar kasancewa ɗan ƙasa guda biyu.

Atiku ya ce Tinubu ya ƙi bayyana cewa yana da takardun shaidar zama ɗan wata ƙasar ban da Najeriya a fom ɗin EC9, da ya cike.

Ya zarge shi da zama ɗan Najeriya da kuma mallakar takardar ɗan ƙasa a Guinea.

Sai dai, ɗaya daga cikin alƙalan kotun yayin gabatar da hukunci a kan wannan ƙorafi, Mai shari’a Moses Ugo ya ce wannan ba matsala ce da za ta hana Tinubu takara a Najeriya ba.

Don haka kotun ta yi watsi da wannan ƙorafi.

Haka zalika, Atiku Abubakar ya ambato zargin safarar ƙwayoyi da halasta kuɗin haram a cikin ƙorafe-ƙorafensa. Kotun dai ta sa ƙafa ta shure zarge-zargen su ma.

Aringizon ƙuri’u

Atiku Abubakar ya kuma ce ana iya soke nasarar Tinubu saboda aringizon ƙuri’un da aka yi a jihojin Kano da Lagos, sai dai kotun a nan ma ta yi watsi da buƙatar.

Ta kafa hujjar cewa mai ƙorafin bai shigar da Rabi’u Musa Kwankwaso da Peter Obi cikin waɗanda yake ƙara ba. A cewarta, su ne suka samu ƙuri’u mafi rinjaye a jihohin da Atiku ya nuna jayayya a kansu.

Shi ma, Peter Obi ya nemi a soke nasarar shugaban ƙasar bisa zargin aringizo a jihohi masu yawa na Najeriya ciki har da Yobe da Kano da Oyo.

Kotun dai ta ƙi amincewa da iƙirarin, ta ce masu iƙirarin ba su gabatar da bayani a kan haƙiƙanin tasoshin zaɓen da aka yi aringizon ba.

“Hankali ba zai ɗauka ba a ce, mai ƙorafi ya yi zargin maguɗi a wurare masu yawa cikin tasoshin zaɓe 176,000 na mazaɓu sama da 8000 da ke ƙananan hukumomi 774 a cikin jiha 36 da kuma Abuja, amma ba tare da ya fayyace taƙamaimai wuraren da aka yi maguɗin da ya yi zargi ba,” kotun ta ce.

Jam’iyyar LP ta kuma yi zargin cewa hukumar zaɓe ta rage mata ƙuri’u, inda ta ƙara wa jam’iyyar APC.

Kotun a nan ta ce LP ta gaza yin cikakken bayani a kan taƙamaimai adadin ƙuri’un da ta ci, kafin a rage mata su, da kuma tashoshin zaɓen da hakan ta faru.

Akwai shaidar mutum 13 da aka fara gabatarwa, waɗanda suka yi iƙirarin cewa sun ga maguɗin zaɓen da aka yi a kan idanunsu, mutum 10 a ciki sun ce zaɓe ya tafi daidai babu wata matsala, sai dai kan yadda aka aika sakamako ta laturoni, hujjar da alƙalan suka yi watsi da ita.

‘Mutum ɗaya, takara biyu’

Jam’iyyar APM, ta nemi a soke cancantar zaɓen Bola Tinubu da Kashim Shettima.

Ta yi ƙorafin cewa an ba da sunan Kashim Shettima, don tsayawa takara kan muƙamai guda biyu a lokaci ɗaya.

APM ta ce an fara bayar da sunan Kashim a matsayin ɗan takarar sanata a mazaɓar Borno ta Tsakiya kuma daga bisani aka tura sunansa ga hukumar zaɓe don tsayawa takarar mataimakin shugaban Najeriya.

Lokacin da yake karanto hukunci, Mai shari’a Tsammani ya ce, ƙorafin APM matsaloli ne da suka faru gabanin zaɓe, kuma kotunsu ba ta da lokacin sauraren irin wannan ƙarar. Ya ce batun hurumi ne na babbar kotun tarayya.

Kuma a cewarsa idan za a kai ƙara kotun tarayyar, za a yi hakan ne cikin kwana 180 da bayar da sunansa kamar yadda doka ta tanada, da zarar kwanakin sun wuce, to babu dalilin sauraren ƙorafin.

Tsammani ya ƙara da cewa batun ba hurumin APM ba ne, domin kuwa tsayar da ɗan takara, matsala ce ta cikin gida a jam’iyyar APC.

APM ta yi zargin shi kansa Bola Tinubu bai cancanta ba, abin da Mai shari’a Tsammani ya ce da sun sani da sun tafi kotu cikin kwana 14 na farko bayan ayyana shi a matsayin ɗan takarar jam’iyyar APC.

Ya ƙara da cewa a tsarin mulkin Najeriya sashe na 131 zuwa na 137, duk inda aka yi zaɓe aka ayyana wanda ya lashe zaɓen, maganar cancantar ɗan takara ba za ta taɓa zama cikin batutuwan da za a ƙalubalance su ba a kotu.

Shugaba Tinubu na Najeriya dai ya yi maraba da wannan hukunci da kotu ta yanke, cikin wata sanarwa da ya fitar jim’kaɗan bayan kammala hukuncin.

Shi ma, mutumin da ya gada, tsohon shugaban ƙasar Muhammadu Buhari ya yaba da hukuncin. Yayin da ‘yan adawa ke cewa suna nazari a kan mataki na gaba da za su ɗauka bayan sun ce ba su yarda da matsayin alƙalan kotun ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here