Lionel Messi da Erling Haaland na daga cikin wadanda za su fafata neman zama gwarzon duniya da zai lashe kambun Ballon d’Or na bana.
A gefe guda kuwa, tauraruwar gasar cin kofin duniya ta Spain, Aitana Bonmati, ke jagorantar wadanda aka zaba a ranar Laraba don samun lambar yabo ta mata.
Messi, wanda kwanan nan ya raba gari da kungiyar kwallon kafa ta PSG zuwa Inter Miami, yana cikin jerin ‘yan wasan da aka zayyano tare da Karim Benzema.
Messi na iya samun damar lashe Ballon d’Or karo na takwas, bayan rawar da ya taka wajen jagorantar Argentina wajen lashe gasar cin kofin duniya da aka yi a Qatar a bara.
Haaland na iya zama babban abokin hamayyarsa wajen lashe kyautar bayan ya zura kwallaye 52 a wasanni 53 da ya taimaka wa Manchester City ta lashe gasar zakarun Turai da Firimiyar Ingila da kuma kofin FA a kakar wasan da ta gabata.
Dan wasan gaba na Norway, a makon da ya gabata ya lashe kyautar gwarzon dan wasan UEFA na shekarar da ta gabata.
Dan wasan gaban PSG, Kylian Mbappe da Haaland da Kevin de Bruyne, na daga cikin ‘yan wasa 30 da aka zaba don lashe kyautar.
Za a yi bikin ba da kyautar a birnin Paris na kasar Faransa a ranar 30 ga watan Oktoban wannan shekara.
Ga jerin sunayen ’yan wasa 30 da aka zabo domin lashe kyautar:
- André Onana – Manchester United/Kamaru
- Josko Gvardiol – Manchester City/Croatia
- Karim Benzema – Al Ittihad
- Jamal Musiala – Bayern Munich/Jamus
- Mohamed Salah – Liverpool/Masar
- Jude Bellingham – Real Madrid/Ingila
- Bukayo Saka – Arsenal/Ingila
- Randal Kolo Muani – Paris Saint-Germain/Faransa
- Kevin De Bruyne – Manchester City/Belgium
- Bernardo Silva – Manchester City/Portugal
- Emiliano Martínez – Aston Villa/Argentina
- Khvicha Kvaratskhelia – Napoli/Georgia
- Rúben Dias – Manchester City/Portugal
- Nicolo Barella – Inter Milan/Italy
- Erling Haaland – Manchester City/Norway
- Yassine Bounou – Al Hilal/Moroko
- Martin Ødegaard – Arsenal/Norway
- Julián Álvarez – Manchester City/Argentina
- Ilkay Gündogan – Barcelona/Germany
- Vinícius Júnior – Real Madrid/Brazil
- Lionel Messi – Inter Miami/Argentina
- Rodri – Manchester City/Spain
- Lautaro Martínez – Inter Milan/Argentina
- Antoine Griezmann – Atletico Madrid/Faransa
- Robert Lewandowski – Barcelona/Poland
- Kylian Mbappé – Paris Saint-Germain/Faransa
- Kim Min-Jae – Napoli/South Korea
- Victor Osimhen – Napoli/Najeriya
- Luka Modric – Real Madrid/Croatia
- Harry Kane – Bayern Munich/Ingila