Hakikanin gaskiya kan bullar mata masu shan jini

0
223

Tun daga karshen watan Agusta aka rika yada jita-jitar bayyanar wasu mata da suke shiga gidajen mutane wadanda ake musu lakabi da ‘masu shan jini’ a wasu sassa na Arewa musamman Jihar Kano.

An ce wadannan mutane suna yawo ne gida-gida a lokacin da ska tabbatar da mazaje ba sa gida, inda da zarar sun shiga, abin da suke fara nema shi ne a taimaka musu da ruwan sha ko wani abu, wanda kuma da an taimaka musu da abin da suka bukata, to wacce ta ba da taimakon sai a ga ta yanke jiki ta fadi, daga nan lamarin ya kai ga ta rasa ranta.

Masu yada maganganun sun ce irin wannan ibtila’i ya faru a unguwanni daban-daban a cikin Birnin Kano.

A wasu bidiyo da suke yawo a kafofin sadarwa na zamani ana ganin yadda ake dukan wadannan mata yayin da aka kama su, sannan kuma a lokacin da ake yi musu tambayoyi sukan kasa ba da wata gamsasshiyar amsa da za ta fahimtar da mutane yadda gaskiyar lamarin yake.

An samu irin wannan lamarin a unguwannin Hotoro, Zango, Rijiyar Lemo, Gwagwarwa, Kwana Hudu Medile, da sauran wasu unguwanni da ke cikin birnin Kano.

Baya ga haka, akwai wani bidiyo da yake yawo na wasu mata ‘yan kauye da aka nuna wasu matasa na yi musu tambayoyi, amma su kuma maganarsu ba irin ta ‘yan Jihar Kano ba ce mutanen Sakkwato ne.

Sannan akwai wani bidiyo na wata baiwar Allah da lamarin ya shafi ‘yarta wacce ‘yar ba ta kai shekara guda da haihuwa ba, inda uwar take bayanin yadda ta rasa ‘yarta ta irin wannan hanya.

Wakazalika, akwai wata murya da take yawo a zaurikan WhatssApp, inda wani yake jan hankali mutane su yi hankali da wasu mutane da suke tura wa mutane wasu lambobi 155-155, inda mai muryar ya ce “bayan an tura maka wadannan lambobi sai wani ya kira ka daga baya yana gaya maka cewa “Mahaifinmu ya yi kuskuren tura maka katin waya, don Allah turo min su idan ka gans u. Bayan ka tura masa, sai ya tura wa wanda ya ce shi ne mahaifin nasa lambarka, sai ya gaya maka cewa yanzu baban namu zai kira ka, to daga nan ne za ka ji an kira ka, idan ya kira, sai ya ce ka rufe idanunka zai yi maka addu’a ka rika cewa amin, da zarar ya fara kana cewa amin kawai za ka yanke jiki ka fadi, shike nan sun bayar da jininka,” in ji shi.

Akwai bidiyo irin wadannan wajen guda bakwai da har yanzu suke yawo a kafofin sada zumunta.

Kamar yadda  LEADERSHIP Hausa ta bi diddigi, tun da farko daga yankin Kankara da ke Jihar Katsina aka fara samun bullar irin wannan labari, inda aka ce wata tsohuwa ta shiga wani gida inda ta bukaci a taimaka mata da ruwa ta shiga ban daki, shigarta ke da wuya sai matar gidan ta fadi. A cewar labarin sai jini ya fara kwarara daga jikin matar, daga nan sai ita bakuwar ta kama hanyar ficewa daga gidan a kan hanyar fita suka ci karo da mijin matar, tun da bai san abin da ke faruwa ba sai ya bar ta  ta wuce, yana shiga gida sai ya tarar da matarsa cikin jini, hakan tasa ya dawo da gudu, ya nemi gudunmawar al’umma aka kama matar. Bayan yi mata tambayoyi sai ta bayyana cewa su 100 aka turo Jihar Katsina, yanzu haka an kashe tara daga cikinsu, ita ce ta goma. In ji majiyarmu.

A Kano ma an samu irin wannan labari a unguwar Gadon Gaya. Inda nan ma wani magidanci ya ce matarsa ta yi masa waya yana kasuwa, ta sanar da shi cewar wata mata ta kwankwasa gidansa kuma matarsa ta bude kofar tsakiya inda bakuwar ta bangaje ta tana kokarin shiga gidan, sai matarsa ta rufe kofar tsakiya, wai a cewar labarin, matar da bakuwarta suka leko ta saman gidan suka ji ita wancan mata na amsa waya tana cewa ai sun ma rufe gidan sun hana ta shiga cikin gida.

A unguwar Hotoro ma da safiyyar Asabar da ta gabata an ce wai wata tsohuwa ta hadu da wata yarinya ‘yar kimmanin shekara goma zuwa sha biyu dauke da yaro a hannunta dan kimanin shekara daya a duniya, sai wannan tsohuwa ta dafa kan yaron, kawai sai yaro ya fara kakkafewa kafin ka ce kobo wasu mutane da ke can gefe suka ankara tare da  da kai dauki, nan da nan  tsohuwar ta ranta a na kare, an samu nasarar damketa aka kuma mikata ofishin ‘yan banga da ke Hotoro. Amma dai a cewar labarin bayan kai yaron asibiti daga baya rai ya yi halinsa

Haka lamarin ya faru a unguwar Kwana Hudu, Sheka Sabuwar Abuja da ke yankin Karamar Hukumar Kumbotso da ma wasu wurare.

Sakamakon yadda lamarin ya yi kamari a tsakanin al’umma, LEADERSHIP Hausa ta gudanar da Shirin Tattaunawa ta Manhajar Twitter Space, inda ta gayyato mai magana da yawun ‘yansanda, reshen Jihar Kano, SP Haruna Abdullahi Kiyawa da kwararriyar mai horarwa da warware mishkilar zamantakewa, shugabar Cibiyar Nurul Huda, Hajiya Binta Shehu Bamalli domin warware zare da abawa kan wannan al’amari.

A jawabin da ya yi, SP Haruna ya tabbatar da wannan jita-jita da ake yadawa inda ya ce tuni rundunarsu ta kaddamar da bincike, yana mai cewa, “Mun samu rahotanni 14 cikin kwana 5 na rufar wa mata da zargin ‘yan shan jini ne, kamar a unguwar Hotoro an samu guda uku, Zango 4,” in ji shi.

Sannan ya ce Rundunar ‘Yansandan Jihar Kano ta yi nasarar kama mutum takwas da ake zargi da dukan irin mata da ake zargin masu shan jini ne inda za a tasa keyarsu zuwa gaban kuliya ba da jimawa ba.

“Duk mun gudanar da bincike daya bayan daya, duk binciken da muka yi ba mu samu ko daya a cikin matan da ake zargi da laifin shan jini ba, abu ne na Allah wadai. A Unguwar Kwana 4, wasu ‘yan mata ne suka kai caji a wani gida, kawai daya ta ce wa matar gidan za ta je bandaki sai matar ta kwarma ihu wai budurwar ‘yar shan jini ce, shi kuma maigida da ya zo maimakon ya yi amfani da hankali kawai sai ya kulle ‘yan matan a daki,’yan unguwa suka taru, matar gidan ta daki wadda take zargin, ‘yansanda ne suka kubutar da su.

“Mun samu wannan a Dawakin Tofa, wata tsohuwa ce daga neman taimako kawai shi ma wani ya ce ‘yar shan jini ce. Haka abin ya rika faruwa da masu bara da ‘yan talla. Wata kawai tana tallar turare ne, da yake bakuwa ce a unguwar sai kawai wata mata ta kalle ta, ta ce ta shanye wa danta jini, da aka kai yaron asibiti sai aka gano maleriya ce mai karfi ta kama shi, ana yi masa allurai yaro ya farfado. Haka nan a karamar hukumar Rano mun samu rahoton aukuwar lamarin.” In ji shi.

SP Haruna ya yi kira ga mazauna Kano da su yi watsi da irin wannan jita-jita da ake yadawa a tsakanin al’umma. Ya kara da cewa, “Mun gudanar da bincike a kansa kuma mun gano babu kamshin gaskiya a cikinsa, an kirkiri wannan jita-jita ce kawai domin  cusa tsana ga matafiya ko baki a Kano wanda hakan kuma ke iya kaiwa ga tada hankulan al’umma, da cusa tsoro, rikicin gangan wanda zai kawo cikas ga kyakkyawan zaman lafiyar da al’ummar Kano ke kwankwada.”

Ya bayyana cewa a halin yanzu rundunarsu na kokarin zama da malamai domin su wayar da kan jama’a game da wannan lamari ta hanyar gabatar hudubobi ga jama’a a masallatai.”

A nata bangaren, Shugabar Cibiyar Horarwa ta Nurul Huda, Hajiya Binta Shehu Bamalli ta yi bayanin cewa,

“Ana ta yadawa muna ganin bidiyos, ana ce wa mutane a daina ba da taimakon ruwan sha kuma a daina bude kofar gida. Gaskiya kowane Dan’adam akwai yakininsa. Da aka fara yadawa, na ce wannan tsafi ne amma ni ban yarda da shi ba. Na daya dai, mu mata daga mahangar addini, Allah ya umarci Manzon Allah SAW ya fada wa muminai a killace mata a gida. Kuma haka nan mata a yanzu ana business ana aiki amma ya kamata a yi bisa sharuddan addini. Abin da ya sa abin ya fi faruwa da mata saboda mu ne muke da sakaci, Wasu make-up da ake yi mara ma’ana, to mai yin irin wannan ne ma abin zai iya kamata. Sannan an manta da yin azkar da addu’o’i shi ya sa ma idan an yi abin zai kama mutum.

“Ni dai ban yarda da abin ba dama. Ba na jin akwai wanda zai zo ya ce na ba shi ruwa na hana shi. Idan ka ciyar ko ka shayar Allah zai ba ka lada. To don me za a hana mutane yi? Ni da nake son yin taimakon saboda Allah ba na tunanin wani abu zai faru in ba alheri ba. Ya kamata mu koma wa wayewar addinin musulunci ba na bature ba kawai. Idan kuma kina azkar wani abu ya faru to ka sani wannan jarrabawa ce kawai. Kuma Allah na iya sa haka ta zama kaffara.” In ji ta.

Haka nan ta yi kira ga mutane su daina yada abubuwa marasa kyau, tana mai cewa, “abin ko da gaskiya ne yada shi ba shi da amfani. Akwai wadanda da gaske suna neman taimko kuma ba miyagu ba ne amma sai a yi musu ihu a ce suna cikin abin, ka ga za a yi ta daukar alhakin mutane. A mtsayinmu na al’umma mu dinga yi wa kanmu adalci a kan komai. Mu dinga yin bincike da aunawa a ma’aunin hankali kan komai da muke yadawa”

Har ila yau, da suke tofa albarkacin bakinsu, mutanen da suka halarci shirin sun yi kira a kara ta-ka-tsan-tsan da ire-iren abubuwan da suke faruwa.

Muhammadu Garba Dogo, Dan’amar na Azare daga Jihar Bauchi, ya bayyana cewa, “Akwai wata mata da aka ji wa ciwo a Bauchi a kan tana daya daga cikin wadannan mata, gaskiya ko da na ga bidiyon abin da aka yi mata, sai na yi wa iyalaina da ke Maidile a Kano magana cewa su rufe gida, idan mutum ya kwankwasa a tambaya waye kafin a bude. Saboda idan irin wannan abu yana faruwa, ba za ka ce gaskiya ne ko karya ne ba, amma ya kamata ka dauki mataki. Na Bauchi na samu gamsasshen bayani cewa mata ce tana da dan tabin-hankali, to ta je tana neman taimako sai aka yi mata wannan aika-aika… Sannan zancen masu kiran waya, ni ma an yi mun shekara biyu da suka wuce, sannan kwanan nan ma akwai wanda ya kira ni, yana fara magana na dakatar da shi. Sannan masu tura kati su ma sun yi mun, sun turo da lambar na tura musu har ya hada ni da Baban nasa sun kira ni suka fara wannan maganganun nasu su ma na kyale su, to ni dai ina kira ga mutane kowa ya saki jiki sannan mu yi hankali da masu shirin tayar da hankula.”
Shi ma da yake ba da gudunamarsa, Malam Usman, ya ce “A Arewa musamman a karkara ana samun tsofaffi da ba sa aikin komai sai shiga gidaje suna roko, to idan suka taba yaro sai ya shiga wani hali. Yanzu ya kamata kowa ya kara tsaurara tsaro a gidansa, a daina barin yara suna wasa a kofar gida, abubuwa sun canja, matasa na iya yin komai a kan kudi. A ci gaba da wayar da kan mutane kuma Alhah ya tsare mu.”

Haka nan wani dan jarida da ya shigo cikin shirin daga Gombe, Sani Musa, ya bayyana cewa, “Tun a makon da ya gabata muna ganin abubuwa iri-iri. Irin wannan tattaunawa a shafukan sadarwa yana da kyau domin wayar da kan al’umma. Wannan harka ta asiri a wani bincike da na yi, na gano abin ya taso ne daga kudu inda aka ce wasu ‘yan kungiyar asiri sun ware Naira miliyan 360 domin shigar da mutane kungiyoyin tsafi, kuma idan suka samu mutane ba Imani sai su ribaci mutum. Don haka kowa yad ai ya kiyaye.”

Shi kuwa, Mustapha Nuhu daga Kano, cewa ya yi, “Duk yawancin abubuwan da muke gani kashi 99 cikin 100 duk karya ne. An bijiro da abin ne domin dakile mabarata. Lokacin Korona an so a yi haka, mutum zai ga abu a socil media ba zai yi bincike ba kawai sai ya yada. An turo mun wani bidiyo, mai maganar ciki kamar yare ne amma a ciki yana cewa wai a Katsina aka yi. Ina ba da shawara mutane mu tsaya da azkar, ana cikin wani hali, Allah ya tsere mu.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here