‘Yan ta’adda sun hallaka mutum 64 a Mali

0
287

Mayaka masu kaifin kishin Islama sun kai hari kan wani jirgin ruwa a yankin arewa maso gabashin Mali, inda suka hallaka fararen hula akalla 49, in ji gwamantin riko kwarya ta kasar.

Gwamatin ta kuma bayar da rahoton cewa, mayakan sun kai hari kan wani sansanin sojoji, inda suka kashe sojoji 15, yayin da suka ce an hallaka mayaka kusan 50.

Gwamnatin kasar ta ayyana zaman makoki na kwanaki uku.

Barazanar da ake fuskanta daga ma su kaifin kishin Islama na karuwa duk da ikirarin da sojoji suka yi na cewa sojojin haya na kamfanin Wagner na kasar Rasha sun karya lagwonsu.

Tun a karshen watan daya gabata ne birnin Timbuktu da ke arewaci aka yi masa kofar rago kuma an kai hare hare da dama a baya baya nan kan harkokin sufuri.

BBC ba ta samu wata majiya mai zaman kanta da ta tabbatar da rahoton gwamnatin kasar na baya baya nan ba, wanda aka karanta a gidan talibijin na gwamnati.

Rahotanni sun ce mayakan sun kai wa jirgin ruwan hari ne a lokacin da yake tafiya a cikin kogin Nijar daga garin Gao zuwa Mopti.

‘Yan ta’addarr sun kuma kai wa wani sansanin sojoji hari da ke Bourem Circle a yankin Gao.

Tun a shekarar 2020 sojoji ke mulki a kasar ta Mali.

Sojojin sun sami gagarumin goyon bayan jama’a a lokacin da suka yi juyin mulki bayan zanga zangar kin jinin gwamnatin Ibrahim Boubacar Keita shekaru uku da suka gabata.

Mutane sun fusata saboda durkushewar tattalin arziki da zaben da aka rika takadama akai da kuma matsalar rashin tsaro.

Tun bayan wannan lokaci bincike ya nuna cewa gwamnatin sojin Mali ba ta tabuka wani abin a zo a gani ba a fadan da ta ke yi da mayaka ma su tayar da kayar baya da ke rike da wasu sassan kasar.

A watan da ya gabata ne kungiyar da ake kira the Support for Islam and Muslim watau GSIM ta sanar cewa za ta rufe duk hanyoyin da ke jihar Timbuktu mai fama da tashin hankali tun shekarar 2012 sakamakon boren da mayakan Abzinawa suka yi a arewacin kasar.

Sai dai matsalar tsaron ta yi kamari ne bayan mayaka masu ikirarin jihadi su ka kai hari cikin kasar da Nijar da kuma Burkina Faso a 2015.

A 2015 ne gwamnatin kasar ta yi sulhu da mayakan abzinawa ma su tayar da kayar baya a arewacin Mali amma yarjejeniyar da aka cimma ta fuskanci cikas bayan da sojojin suka yi juyin mulki.

An shiga cikin wani yanayi na zaman zulumi bayan Majalisar Dinkin Duniya ta mika wasu sansanoni biyu da ke kusa da Tmibuktu ga dakarun kasar bayan gwamnatin Mali ta bukaceta ta fice daga kasar kafin karshen shekarar da mu ke ciki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here