An kama masu ‘yunkurin juyin mulki’ a Burkina Faso

0
226

Gwamnatin sojin Burkina Faso ta sanar da kame wasu sojoji kan zargin su da yunkurin kifar da gwamnatin kyaftin Ibrahim Traore.

Ofishin babban mai shigar da kara na kasar ya ce sojojin na fuskantar zargin zagon kasa ga gwamnatin Traore da yunkurin juyin mulki.

Sauran zarge-zargen sun hada da na karya dokokin soja da barazana da tsaron kasa da kuma yunkuri jefa rayuwar jama’a cikin hadari.

Ofishin ya ce duk sojojin da ake zargin — biyu na bakin aiki, na ukun ya yi ritaya — sun dauki lokaci suna bibiyar Traore a gidansa da duk wuraren da ya je, haka kuma suke bibiyar makusantansa.

Sanarwar gwamntin ta ce bayan dogon bincike ne aka kame su don amsa tambayoyi domin gano iyayen gidansu.

Ofishin na zargin su da yunkuri na wargaza gwamnatin rikon kwaryar da ke fatan dakile matsalolin tsaron da kasar ke fama da su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here