Hotuna: Girgizar kasar Morocco

0
304

Girgizar kasar da ta faru a Maroko ta fi shafar birnin Marrakesh mai dimbin tarihi, wanda UNESCO ta ayyana a cikin wuraren tarihin duniya.

Alkaluma sun nuna cewa kawo yanzu mutum 1037 ne suka mutu, galibinsu a yankunan karkara da ke wahalar zuwa.

Hukumomin Maroko sun ce girgizar kasar tana da karfin maki 7.0.

Ta fi shafar yanki mai nisan kilomita 75 da ke kudancin Marrakech, sannan zurfinta ya kai kilomita 18.5.

Bidiyoyin da aka wallafa a soshiyal midiya sun nuna yadda mutane suka warwatsu a kan tituna cikin yanayi na kidimewa.

Shugabannin kasashen duniya sun aika da sakonnin ta’aziyyarsu da goyon baya ga kasar Maroko bisa aukuwar girgizar kasar da wasunsu suka bayyana a matsayin “mai matukar muni”.

Lamarin ya jefa kasar cikin jimami da alhini musamman ganin cewa girgizar kasar ta faru ne da daddare lokacin mutane na tsaka da barci.

Cibiyar nazarin yanayi ta ce girgizar kasar ita ce mafi karfi da Maroko ta taba fuskanta.

An yi kalarta a Algeria da Mauritania.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here