Manoma na farin ciki sakamakon tashin farashin agushi a Taraba

0
98

Manoman Agushi a Jihar Taraba, na cikin murna da farin ciki sakamakon tashin gwauron zabi da farashinsa ya yi a kasuwannin jihar.

Bincike ya tabbatar da cewa, buhun Agushin mai nauyin kilo 100, ana sayar da shi a kan farashin Naira 100,000.

Har ila yau, binciken ya sake tabbatar da cewa, baya ga tashin farashin nasa, manoman sun sake samun amfani mai dimbin yawa bayan sun girbe shi a Jihar ta Taraba.

Bugu da kari, a gona daya tak an girbe buhu kimanin goma a shekarar da ta gabata, sama da buhu 25 aka girbe a irin wannan gonar.

Daruruwan manoman a garuruwan Bali, Gassol, Gashaka, Donga da kuma Karim-Lamido da ke a Karamar Hukumar  Wukari ta Jihar Taraba, akasari sun rungumi yin noman Agushin, sakamaon karin bukatarsa da ake yi a ‘yan shekarun nan.

An rawaito cewa, wasu daga cikin manoman a garuruwan Bali da Gassol, sun girbe sama da buhu 100 na Agushin a kakar nomansa ta bana, wanda hakan ya sa suka samu miliyoyin nairori a matsayin kudin shiga.

Sakamakon  samun irin wannan gagarumar riba ne, wasu manoma da dama a jihar, su ma suka fara yin wannan noma na Agushi, wanda a cikin watanni uku kacal masu zuwa suke sa ran fara girbe shi.

Daya daga cikin manoma Agushin mai suna Musa Saidu, ya sanar da cewa, a shekarar da ta gabata, ya girbe kimanin buhu 60, inda kuma a kakar noman bana ya girbe buhu 95, duk dai a cikin wannan gonar tasa.

Haka zalika, Musa ya kara da cewa, Agushi na samun karbuwa a daukacin kasuwannin da ke cikin Jihar Taraba, ya kuma kara da cewa, a kasuwannin Garba, Chede Maihula da kuma sauran kasuwanni, akwai dillalansa daga sassa daban-daban na wannan kasa.

Har ila yau, bincike ya nuna cewa, shi kansa Iri na Agushin kala biyu ne wanda aka fi bukata, wadanda kuma ake sayar da su da matukar tsada, sannan ya sanar da cewa, Iri na samfurin China ana kara nuna bukatarsa, wanda a yanzu ya buhu mai cin kilo 100, ya kai daga naira   90,000 zuwa Naira 100,000.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here