Tinubu ya amince a gina gidaje 1,000 a jihohin arewa 7 – Shettima

0
330

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya bayyana cewa, shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da gina gidaje 1,000 a jihohin Sokoto, Kebbi, Katsina, Zamfara, Kaduna, Neja da Benuwe a wani babban shiri na gwamnatin tarayya na tallafawa jihohin da kalubalen rashin tsaro ya addaba a yankin Arewa.

Shettima, wanda ya wakilci shugaba Tinubu, ya bayyana hakan ne da yammacin ranar Juma’a a Maiduguri, babban birnin jihar Borno, yayin kaddamar da ayyukan da gwamnatin jihar Borno ta aiwatar a cikin kwanaki 100 na gwamnatin Gwamna Umara Zulum.

A cewarsa, cikin wata sanarwa da ofishin yada labaran ofishin mataimakin shugaban kasa ya fitar, ya bayyana cewa, “shugaban Tinubu ya amince a baiwa hukumar bada agajin gaggawa ta kasa (NEMA) Naira biliyan 50 don fara aiwatar da shirin Pulaku – wani shirin tallafi ga al’ummar yankin arewa maso yamma da matsalar tsaro ta addaba.

“Shugaban kasa ya amince da gina gidaje 1000 a Sokoto, Kebbi, Katsina, Zamfara, Kaduna Neja da Benuwe, wanda za a gina dukkan sauran kayayyakin more rayuwa acikinsu, kamar makarantu, Asibitoci, Asibitin dabbobi da wuraren kiwon dabbobi ga al’ummar fulani da ke yankin.”

Ya kara da cewa, dukkan sassan kasar nan za su ci gajiyar shirye-shirye na ci gaba da shugaba Tinubu ke kudurin aiwatarwa, ya kuma bayyana cewa, gwamnatin tarayya na shirin sake farfado da noman alkama a kasar nan.


Da yake jawabi, mataimakin shugaban kasar ya bayyana cewa, shugaba Tinubu na sane da kalubalen da ‘yan Nijeriya ke fuskanta kuma zai yi kokarinsa wajen samo mafita.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here