‘Yan kungiyar asiri sun hallaka DPO a Ahoada-Gabas dake Ribas

0
102

Wasu da ake zargin ‘yan kungiyar asiri ne, a daren Juma’a, sun kashe jami’in ‘yan sanda (DPO) Bako Angbashim, mai kula da sashin ‘yan sanda na Ahoada da ke karamar hukumar Ahoada- Gabas ta jihar Ribas.

Angbasim, Sufeton ‘yan sanda, shi ne DPO mai kula da sashen ‘yan sanda bangaren kungiyoyin asiri kafin a mayar da shi Ahoada-Gabas, don ya taimaka wajen shawo kan matsalar rashin tsaro da ayyukan kungiyoyin asiri ke yi a kananan hukumomin Ahoada- Gabas da Ahoada-Yamma na jihar.

An rawaito cewa babban jami’in ‘yan sandan da aka hallaka ya mutu ne a yayin wani artabu tsakanin jami’an ‘yan sanda da wasu da ake zargin ‘yan kungiyar asiri ne da ke unguwar Odeimude a karamar hukumar Ahoada- Gabas.

Jami’ar hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan (PPRO), Grace Iringe-Koko, a wata sanarwa da ta fitar a safiyar ranar Asabar, ya ce daya daga cikin jami’ansu da suke tare da DPO da aka hallaka shi ma ya samu rauni a yayin artabun wanda a halin yanzu yana samun kulawar likitoci a asibiti.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here