Biden ya jinjina wa Tinubu kan shugabancin Ecowas

0
76

Shugaban Amurka Joe Biden ya yaba wa takwaransa na Najeriya Bola Tinubu kan ƙarfin shugabanci a matsayinsa na shugaban Ƙungiyar Tattalin Arzikin Ƙasashen Afirka ta Yamma Ecowas.

Mista Biden ya jinjina wa Tinubu a ƙoƙarinsa martaba tare da kare dimokraɗiyya a jamhuriyar Nijar da yankin Afirka ta Yamma.

Ofishin jakadancin Amurka a Najeriya ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa Shugaban na Amurka ya gana da Tinubu a gefen taron ƙungiyar G-20 ta kasashe masu karfin masana’antu da aka gudanar a birnin Derkhi na kasar Indiya.

An yi ganarwa ne domin jaddada goyon bayan Amurka ga Najeriya, kamar yadda ofishin jakadancin Amurkan a Najeriya ya bayana.

“Shugaba Bide ya jinjina wa gwamnatin Tinubu bisa matakan da ta ɗauka na gudanar da sauye-sauyen tatalin arziki, sannan ya gode wa Shugaba Tinubu bisa jajircewar da ya nuna a matsayinsa na shugaban ƙungiyar Ecowas wajen kare tare da tsare dimokradiyya a Nijar da ma yankin yammacin Afirka,” kamar yadda fadar gwamnatin Amurka ta ‘White House’ ta bayyana .

Ta kara da cewa ”gayyatar da aka yi wa Najeriya zuwa taron G-20 alama ce irin martabar da ƙasar ke da ita a idon duniya, a matsayinta na giwar dimokraɗiyya da tattalin arziki a duniya“.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here