Borussia Dortmund ta fara shirin dauko dan wasan Manchester United, Jadon Sancho, mai shekara 23, a watan Junairun badi idan ba su daidaita da manajan kulub din Erik ten Hag ba.
Arsenal na shirin ci gaba da tattaunawa da dan wasan tsakiya na Norway Martin Odegaard, mai shekara 24, kan sabon kwantiragi.
Real Madrid na zawarcin matashin dan wasan tsakiya na Argentina mai shekara 23, wato Julian Alvarez daga Manchester City.
Daraktan wasan Pro League na Saudiyya, Michael Emenalo ya ce ba za su rufe kowacce kofa a kokakarin da suke yi, na dauko mai kai hari na Masar da ke taka leda a Liverpool, wato Mohamed Salah, mai shekara 31 ba.
Al-Ittihad na zawarcin mai kai hari na Brazil, da ke taka leda a Tottenham wato Richarlison. Ta na son daukar dan wasan ne a matsayin wanda zai cike gurbin dan wasan Masar Muhammad Salah, bayan rashin nasara a cinikin dan wasan kan farashin fam miliyan 150.
Dan wasan tsakiya na Sifaniya, mai taka leda a Manchester City Rodri, mai shekara 27, ya ce ya kamata hukumomin tamaula su dauki mataki kan yadda Pro League din Saudiyya ke kwasar ‘yan wasa.
Chelsea na kokarin kara ‘yan wasan tsakiyarta karfi, da zarar an bude kasuwar saye da saida ‘yan wasa a watan Junairun 2024.
Chelsea har ta fara hararo mai kai hari na Ingila Brentford’s Ivan Toney, mai shekara 27. Da dan wasan Aston Villa Ollie Watkins – da dan wasan gaba na Slovenia Benjamin Sesko, mai shekara 20.
Manchester City na tuntuba kan mai tsaron gida na Sifani da ke taka leda a Barcelona Alejandro Balde, mai shekara 19, tun farkon kakar d muke ciki ta ke kokarin hakan, amma ta dakata saboda ya na kokarin rattaba hannu kan sabon kwantiragi har zuwa 2028.