Sojojin mulkin Nijar sun zargi Faransa da yunƙurin afka wa ƙasarsu

0
173
Tchiani
Tchiani

Sojojin mulkin Nijar sun zargi Faransa haɗa kai da ƙungiyar Ecowas don shirya ƙaddamar da mamayar soji a ƙasar

Hakan na zuwa ne, yayin da sojojin suka kasa cimma matsaya da ƙungiyar Ecowas kan rikicin siyasar ƙasar.

Zargin ka iya tunzura dubban masu goyon bayan mulkin sojin kasar, waɗanda ke gudanar da zanga-zangar goyon bayan sojojin tare da nuna adawarsu ga ƙasar Faransa.

Mai magana da yawun gwamnatin mulkin sojin Kanal Manjo Amadou Abdramane ya ce ‘suna zargin gwamnatin Faransa da shirya dakaru, da kayan yaƙi a wasu makwabatn ƙasar da ke Afirka ta yamma domin afka wa ƙasar.

“Faransa na ci gaba da girke dakarunta a ƙasashe da dama da ke makabtaka da mu, a shirin da take yi na na kawo mana hari tare da mamaye ƙasarmu, wanda shirin haɗin gwiwa ne da kungiyar Ecowas,”kamar yadda ya bayyana a wata sanarwa da ya karanta a gidan talbijin na ƙasar da maraicen ranar Asabar.

Sojojin sun yi iƙirarin cewa faransa ta girke jiragen saman yaƙi, da masu saukar ungulu, da motocin sulke 40 a ƙasashen Cote d’Ivoire da Benin.

Haka kuma sun yi zargin cewa wani ƙaton jirgin ruwa zai kai manyan makamai masu yawa da sauran kayan yaƙi zuwa ƙasshen Senegal da Cote d’Ivoire da kuma Benin.

Ita dai Faransa na ci gaba da tsayuka a kan matsayinta na goyon bayan hamɓararren shugaban ƙasar Mohamed Bazoum, tare da ƙin amincewa da gwamnatin mulkin sojin.

Gwamnatin Faransa ta ƙi amincewa da buƙatar sojojin na janye dakarunta tare da jakadanta da ke ƙasar, a yayin da sojojin suka ce dakarun na Faransa a yanzu na zaune ne a ƙasar ba bisa ƙa’ida ba.

Faransa da Amurka na da sojoji kusan 2,600 a Nijar, a wani ɓangare na yaƙi da masu iƙirarin jihadi a yankin Sahel.

A makon da ya gabata ne Amurka ta sanar da sauya wa wasu dakarunta da ke Yamai matsuguni zuwa sansanin sojin samnat da ke Agadez.

Daruruwan masu goyon bayan juyin mulki a Nijar ne ke taruwa a sansanin sojin Faransa da ke Yamai, suna buƙatar sojojin na Faransa da su fice daga ƙasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here