Yadda ‘yan fashin daji suka yi wa wasu garuruwa kofar-rago a Zamfara

0
313

Mazauna wasu yankunan karkara a jihar zamfara a Najeriya na korafin cewa ‘yan fashin daji sun killace su daga sauran sassan jihar, abin da ya hana su shiga ko fita.

Lamarin ya shafi yankin masarautar Dansadau da ke karamar hukumar Maru inda aka ce ba wanda ke iya kasadar yin tafiya zuwa babban birnin jihar sai da rakiyyar jami’an tsaro, wadda ita ma ba a kullum ake samunta ba.

Wasu hotunan bidiyo da mazauna yankunan suka nada domin sanar da duniya halin da suke ciki sun nuna jerin motocin dakon kaya da kuma na fasinja suna jiran zuwan sojoji domin yi musa rakiya.

A cewar wani mazaunin yankin, an kwashe kusan kwanaki hudu zuwa biyar ba tare da an shiga ko an fita daga yankin ba.

”Abun ya yi muni sosai, tsakanin Dansadau zuwa Gusau tafiya ce ta awa daya, ko miniti arba’in, yanzu idan ka fita sai dai lokacin da ka je ka dawo kawai, tun ranar Litinin da aka fita har yau ba a sake fita ko an shiga ba, sai dai kawai ka yanki shahada ka tafi, ka jefa rayuwarka a hadari” in ji shi.

Ya kara da cewa matsawar mutum ya fita ba lallai bane ya koma, ko dai a halaka shi ko kuma a dauke ka”.

”Wani lokacin a kan yi sati daya ko sati biyu, kafin a samu jami’an tsaron da za su yi wa jama’a rakiya, a cewarsa.

Hon. Abdulmalik Zubairu Bungudu, dan majalisar wakilai daga mazabar Maru da Bungudu inda wadannan yankunan suke, ya tabbatar wa BBC cewa hakan na faruwa tare da kira ga hukumomin tarayya su dauki mataki.

Ya ce matsawar ba a gaggauta daukar matakin da ya kamata ba, za a iya rasa wadannan garuruwan baki daya.

”Ko mara lafiya ake da shi ba a iya kai shi cikin gari don yi masa magani, sai dai a hakura” a cewarsa.

Ya ce ”Zan gabatar da korafi a gaban Majalisa, kowa ya sanh halin da muke ciki, domin a kawo mana dauki”

Sai dai ko da BBC ta tuntubi mai magana da yawun ‘yan sanda a jihar ASP Yazeed Abubakar, ya ce rundunarsu ta kaddamar da wani sabon yunkuri na shawo kan matsalolin tsaron da ke addabar jihar a kowane sashenta.

Kuma in ji shi, wannan aiki na musamman ya fara samun nasara ta yin la’akari da dimbin mutanen da suka kubutar a kwanannan daga hannun ‘yan fashin dajin.

Matsalar tsaro a Zamfara

Jihar Zamfara dai na daya daga cikin jihohin arewa maso yammacin Najeriya da ke fama da hare haren ‘yan bindiga da satar mutane don neman kudin fansa.

Rikicin ya janyo mutuwar mutane da dama da kuma raba wasu da matsugunansu.

Kazalika hare haren ‘yan bindiga kan tilastawa mazauna yankunan jihar zama ba tare da noma gonakinsu ba, abin da mazauna yankunan ke kokawa akai ke nan kullum.

A ko da yaushe mutanen dai su na neman daukin gwamnati a kan wannan matsalar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here