Zaben 2023: Kotun Kano ta kwace kujerar Datti ta baiwa Iliyasu Kwankwaso 

0
172

Kotun sauraron kararrakin zabe ta Majalisar Dokokin Jiha da ke zamanta a Kano ta yi watsi da zaben Yusuf Umar Datti na NNPP bayan gaza yin murabus daga aikinsa a Jami’ar Bayero Kano kwanaki 30 gabanin zaben.

Mai shari’a Ngozi Flora Azinge ta umarci INEC da ta amshi takardar shaidar lashe zabe da aka baiwa Datti a baya tare da ayyana Musa Ilyasu Kwankwaso a matsayin wanda ya lashe zaben da ya samu kuri’u masu rinjaye na biyu a zaben da aka gudanar a 25 ga watan Fabrairu, 2023 a mazabar Kura/Madobi/Garun Malam.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here