Ƙasashen duniya sun tura ma’aikatan agaji zuwa Marocco

0
100

Ma’aikatan agaji daga kasashen duniya sun isa Marocco domin taimakawa takwarorinsu na kasar a aikin ceton wadanda girgizar kasa ta sanya suka makale a baraguzan gini ko tsaunukan da aka gagara isa.

Sama da mutane 2100 ne suka mutu a girgizar kasar ta daren Juma’a.

Gwamnatin Marocco ta ce ta amince da taimakon gaggawar da kasashen Qatar, da Hadaddiyar daular Larabawa da Birtaniya da Sufaniya suka yi.

Daruruwan mutane na ta turuwa asibitico domin bada taimakon jini a Marrakesh.

Manel Houda, ma’aikaciyar asibiti ta ce lamarin ya munana, amma suna baƙin kokarinsu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here