Duk masu amfani da Twitter za su fara biyan kuɗin wata — Musk

0
63

Kamfanin sada zumunta na Twitter ya sanar da shirinsa na fara cazar masu amfani da ƙafarsa kuɗi a kowane wata.

Mai kamfanin, Elon Musk ya sanar da haka ne a lokacin ganawarsu da Fira Ministan Isra’ila, Benyamin Netanyahu.

Elon Musk ya ce cazar masu amfani da kafar X kudin wata-wata ita ce hanyar mafi dacewa wajen daƙile ayyukan masu amfani da butum-butumi wajen gudanar da shafuka a kafar sada zumuntar.

Musk ya sanar da haka ne bayan Netanyahu ya bukace shi da ya ɗauki matakin daƙile ayyukan masu yaɗa sakonnin nuna ƙin jinin Yahudawa a kafar X.

Tun bayan da Musk ya saye kamfanin Twitter a kana Dala biliyan 44, yake ta sauye-sauye a tsare-tsaren kamfanin, ciki har da sallamar dubban ma’aikata da kuma ɓullo da tsarin cazar manyan masu amfani da kafar.

Ya kuma soke tsarin bibiya da kuma toshe miyagun sakonni, da tsarin toshe shafukan da mutum bai don hulda da su, sannan ya buɗe shafukan da aka rufe a baya kan tayar da fitina, ciki har da na tsohon Shugaban Kasar Amurka Donald Trump.

A watan Yuli ne Elon Musk ya sanar cewa kuɗaɗen shigar da kafar X ke samu daga tallace-tallace sun ragu da kusan rabi.

Tun farkon lokacin da Musk ya kawo sauye-sauyensa kamfanonin tallace-tallace suka fara juya masa baya, da zargin sa da mayar da kafar Twitter mara kaidi, da kuma tallata miyagun kalamai da sunan goyon bayan ’yancin bayyana ra’ayi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here