Kamfanin NNPCL ya yi wa manyan ma’aikatansa ritayar dole

0
95

Kamfanin Man Fetur na Najeriya (NNPCL) ya yi wa dukkan manyan ma’aikatansa da ya rage musu kasa da watanni 15 barin aiki ritayar dole.

A Wata sanarwa dauke da sa hannun shugabannin kamfanin mai kwanan wata 18 ga Satumba, 2023 kuma aka wallafa a shafin sada zumunta na X (Twitter) da sanyin safiyar Talata, ta bayyana cewa, ritayar ta fara aiki ne nan ta ke daga ranar Talata 19 ga watan Satumba 2023.

Ta kara da cewa, yanke wannan hukunci ya zama wajibi domin habbaka tsare-tsare da za su kai ga cimma nasarar da kamfanin na NNPCL ke bukata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here