Kotu ta ba da belin ‘yan Najeriyan da ake zargi da halartar auren ‘yan luwaɗi

0
48

Wata kotu a Najeriya ta ba da belin mutum 69 waɗanda aka kama a cikin watan jiya bayan wani samame kan abin da ‘yan sanda suka bayyana da bikin auren ‘yan luwaɗi.

Kamar sauran ƙasashen Afirka da dama, akasarin mutane a Najeriya na kallon luwaɗi da maɗigo a matsayin gurɓacewar tarbiyya.

Ƙasar tana da tsauraran dokoki a kan auren jinsi.

Wani lauyan mutanen da ake ƙra ya ce waɗanda yake karewa za a sake su a matsayin beli amma sai sun ajiye kuɗi kimanin N500,000 kowannensu.

A watan jiya ne, ‘yan sanda suka kama mutanen bayan wani samame a wani otel da ke birnin Warri sakamakon tsegunta musu rahoto game da wnai auren ‘yan luwaɗi.

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan’adam ta Human Rights Watch ta soki lamirin ‘yan sandan Najeriya saboda holin mutanen da ake zargi a bainar jama’a gaban ‘yan jarida, tare da titsiye su kan zarge-zargen da ake yi musu.

Najeriya ta kafa doka wadda ta haramta duk wata mu’amala ta ‘yan luwaɗi, kuma ana iya ɗaure wanda aka kafa laifi tsawon sama da shekara 10 zuwa shekara 14 a gidan yari.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here