Masarautar Katsina ta tuɓe rawanin Hakimin Kuraye kan daurin auren mai HIV

0
76

Masarautar Katsina ta tube rawanin Sarkin kurayen Katsina Hakimin Kuraye Alhaji Abubakar Abdullahi Ahmadu daga sarauta kan wani daurin aure.

Gwamnatin Katsina ta sallami hakimin ne bayan da aka gano cewa daya daga cikin ma’aurata na dauke da cutar HIV.

Sanarwar da Daraktan Yada Labaran gwamnatin jihar ya fitar ta ce gwamnatin ta sallami Sarkin Kurayen Katsina ne bisa shawarar Masarautar Katsina baya samun takardar korafi.

Sanarwar ta ce bayan gudanar da bincike, masarautar ta same shi da laifin jagorantar daurin auren ba tare da bincike da kuma takardun gwajin asibiti ba.

“Bayan samun takardar korafi Majalisar Masarautar ta gudanar da bincike inda ta sami Alhaji Abdullahi-Ahmadu da laifin jagorantar daurin aure ba tare takardun asibiti ba, kamar yadda doka ta tanadar.

“Duk da cewa daya daga cikin ma’auratan na da cutar HIV, basaraken ya jagoranci daurin auren ba tare da bincike ba.”

Takardar sallama daga Sakataren Masarautar Katsina, Alhaji Bello M. Ifo ya aike masa ta ce, “Bisa ga Takardar da Majalisar Mai-Martaba Sarkin Katsina Alh. (Dr.) Abdulmumini Kabir Usman CFR, ta samu daga Ofishin Sakataren Gwamnati mai lamba KTS/SGS/SEC.54/T/7 ta ranar 15/9/2023, a kan maganar daura auren Alhaji Lawal Mamman Auta da Hajiya Halimatu Abdullahi Kuraye, wadda Gwamnatin Jiha ta bada umurnin yi maka ritaya daga Sarautar Sarkin Kurayen Katsina.

“Don haka, Masarautar Katsina ta yi maka Ritaya daga Sarautar Sarkin Kurayen Katsina daga yau Litinin 18/9/2023.

“Da fatan Allah Ya ba mu lafiya da zama lafiya amin.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here