Tinubu ya amince da nadin hadimai 18 ga mataimakin shugaban kasa

0
296

Shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da nadin masu bada shawara da masu taimakawa 18 ga ofishin mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima domin taimakawa wajen cimma manufofin gwamnatin taraya a bangarori daban-daban na bunkasa tattalin arziki.

Tawagar da aka nadan sun hada da mashawarta 6 da masu taimakawa 12 da za su yi aiki a karkashin ofishin Shettima.

Wadanda aka nadan sun hada da: Rukaiya El-Rufai, Tope Kolade Fasua, Aliyu Modibbo Umar, Hakeem Baba Ahmed, Jumoke Oduwole da Sadiq Wanka.

Sauran sun hada da: Usman Mohammed, Kingsley Stanley Nkwocha da Ishaq Ahmed Ningi.

Kazalika akwai, Peju Adebajo, Mohammed Bulama, Kingsley Uzoma, Gimba Kakanda da kuma Temitola Adekunle-Johnson.

Daga cikin jerin Akwai Nasir Yammama, Zainab Yunusa, Mariam Temitope da Bashir Maidugu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here